Amfani da Makami Mai Guba: Amurka Ta Ɗauki Mummunan Mataki kan Wata Ƙasar Afirka
- Amurka ta kakaba wa wata kasar Afirka sababbin takunkumi bayan zargin amfani da makamai masu guba yayin yakin da ake ci gaba da gwabzawa
- Gwamnatin kasar Sudan ta musanta zargin, tana mai cewa babu hujjar da ke tabbatar da ikirarin da Amurka ta yi game da lamarin
- Rahotanni sun ce an yi amfani da iskar chlorine a hare-hare, yayin da Washington ta kara takaita hulɗar tattalin arziki da zirga-zirgar jirage
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da takwas a aikin jarida.
Amurka - Amurka ta kakaba wa gwamnatin Sudan sabbin takunkumi bayan zarginta da amfani da makamai masu guba a yakin da take yi da dakarun Rapid Support Forces (RSF).
Sai dai, rahotanni sun bayyana cewa gwamnatin Sudan ta musanta wannan zargin tare da bayyana shi a matsayin maras tushe.

Source: Getty Images
Amurka ta zargi Sudan
Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta sanar da sabbin takunkumin ne a ranar Litinin, 20 ga Yulin 2026 kamar yadda rahoton The Africa Report ya nuna.
Amurka ta ce gwamnatin Sudan ta karya yarjejeniyar hana amfani da makamai masu guba bayan ta yi amfani da irin wadannan makamai a shekarar 2024.
Sai dai, gwamnatin Sudan mai goyon bayan sojoji ta yi watsi da zargin, tana mai cewa babu wata hujja da ke tabbatar da hakan, tare da zargin Amurka da amfani da siyasa wajen matsa mata lamba, in ji rahoton Sudan Tribune.
Takunkumin da Amurka ta kakabawa Sudan
Sababbin matakan sun hada da kara takaita damar Sudan wajen samun tallafin kudi daga Amurka da kuma hana fitar da wasu kayayyaki zuwa kasar.
Haka kuma, jiragen sama mallakin gwamnatin Sudan za su daina amfani da sararin samaniyar Amurka, matakin da zai kara matsa wa tattalin arzikin kasar lamba.
Amurka ta bayyana cewa ta dauki matakin ne bayan binciken da ya tabbatar mata cewa gwamnatin Sudan ta yi amfani da makamai masu guba a shekarar 2024, abin da ya saba wa yarjejeniyar Chemical Weapons Convention da Sudan ta rattaba hannu a kanta tun shekarar 1999.
Sai dai har yanzu Washington ba ta bayyana inda aka yi amfani da makaman ko kuma ranar da lamarin ya faru ba.

Source: Getty Images
Rahotannin amfani da sinadarin chlorine
Rahotannin da kafafen yada labarai na duniya suka wallafa sun ce sojojin Sudan sun yi amfani da sinadarin chlorine a wasu hare-hare da aka kai a shekarar 2024.
Jaridar New York Times ta ruwaito cewa wasu manyan jami’an gwamnatin Amurka sun tabbatar da cewa shugaban rundunar sojin Sudan, Janar Abdel Fattah al-Burhan, ne ya amince da amfani da chlorine a yakin.
Haka kuma, tashar France 24 ta ce bincikenta ya gano cewa an jefa ganguna biyu dauke da iskar chlorine daga jirgin sama a watan Satumban 2024 a yankin matatar mai ta al-Jaili da ke arewacin Khartoum.
A lokacin, yankin yana karkashin ikon RSF, wadda ke fafatawa da sojojin Sudan tun watan Afrilun shekarar 2023.
An kama mataimakin shugaban Sudan
Tun da fari, mun ruwaito cewa, Shugaban Sudan ta Kudu, Salva Kiir, ya ba da umarnin kama mataimakinsa, Riek Machar, abin da ka iya haddasa sabon rikici.
Manyan kasashen duniya sun fara janye jakadunsu da ma’aikatansu daga Sudan ta Kudu bayan harbe-harbe sun karade Juba, babban birni.
Masana na gargadin wannan rikici na iya jefa Sudan ta Kudu cikin sabon yakin basasa wanda zai yi sanadiyyar asarar dubban rayuka.
Asali: Legit.ng


