Jam'iyyar APC Ta Nesanta Kanta Daga Sunayen Yan Kwamitin Yakin Neman Zaben Gwamnonin Bayelsa, Kogi da Imo

Jam'iyyar APC Ta Nesanta Kanta Daga Sunayen Yan Kwamitin Yakin Neman Zaben Gwamnonin Bayelsa, Kogi da Imo

  • Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta nesanta kanta daga sunayen ƴan kwamitin kamfen na jihohin Bayelsa, Imo da Kogi
  • Jam'iyyar ta bayyana cewa jerin sunayen ƴan kwamitin yaƙin neman zaɓen ba daga gareta suka fito ba
  • Hakan na zuwa ne yayin da ake ta shirye-shiryen tunkarar zaɓen gwamnoni a jihohin guda uku wanda za a gudanar a watan Nuwamba

FCT, Abuja - Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta yi amai ta lashe a ranar Talata, inda ta nesanta kanta daga sunayen ƴan tawagar yaƙin neman zaɓenta a zaɓen gwamnonin jihohin Bayelsa, Kogi da Imo.

Zaɓen gwamnonin na jihohin guda uku dai za a gudanar da shi ne a ranar 11 ga watan Nuwamban 2023.

APC nesanta kanta daga sunayen yan kwamitin yakin neman zabe
Shugaban jam'iyyar APC, Abdullahi Umar Ganduje Hoto: @APCNigeria
Asali: Twitter

Kakakin jam'iyyar APC na ƙasa, Felix Morka, a cikin wata sanarwa ranar Talata da daddare, ya bayyana cewa jerin sunayen ba daga wajen jam'iyyar ya fito ba.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar PDP Ta Bankado Wani Tuggu Da Jam'iyyar APC Ke Kitsawa Kan Fitaccen Gwamnanta

APC ta yi amai ta lashe

Tun da farko jam'iyyar APC ta fitar da jerin sunayen ƴan tawagar yaƙin neman zaɓenta a zaɓen gwamnonin da za a gudanar a jihohin guda uku.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sakataren tsare-tsare na jam'iyyar na ƙasa, Sulaiman Argungu, shi ne ya rattaɓa hannu a cikin jerin sunayen da aka fitar.

A cikin ƴan tawagar yaƙin neman zaɓen na jihar Bayelsa, an ga sunan tsohon gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike, a matsayin mamba.

Wike wanda yanzu shi ne ƙaramin ministan birnin tarayya Abuja, yana cikin ƴan tawagar G5 na jam'iyyar PDP, waɗanda suka riƙa yin fito na fito da jam'iyyar.

Jam'iyyar PDP ita ma ta sanya Wike a cikin sunayen ƴan tawagar yaƙin neman zaɓenta a jihar Bayelsa, inda gwamna Douye Diri na PDP da Timipre Sylva na APC za su fafata a zaɓen gwamna.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Jam'iyyar APC Ta Kara Haddasa Ruɗani a PDP Kan Ministan Shugaba Tinubu

Ana ganin dai wannan aman da jam'iyyar APC ta lashe baya rasa nasaba da rigimar da sanya sunan Wike a cikin jerin sunayen ta janyo.

NNPP Ta Musanta Dakatar Da Kwankwaso

A wani labarin kuma, jam'iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) ta musanta batun cewa ta dakatar da ɗan takararta na shugaban ƙasa, Rabiu Musa Kwankwaso.

Shugaban jam'iyyar NNPP na jihar Kano, Hashimu Dunguruwa, ya bayyana cewa labarin cewa an dakatar da Kwankwaso babu ƙamshin gaskiya a cikinsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel