Babban Layin Wutar Lantarki Ya Samu Matsala ta Farko a 2025? TCN Ya Yi Bayani
- Kamfanin rarraba wuta ya fito ya karyata rahotannin da ake yaɗawa cewa babban layin wuta na ƙasa ya lalace a karon farko bayan shiga 2025
- Mai magana da yawun kamfanin TCN, Ndidi Mbah ya ce rahoton ba gaskiya ba ne, layin da ya samu matsala jihar Legas kaɗai ya shafa
- Mbah ya yi kira ga ƴan Najeriya da su watsi da rahotonnnin da ke yawo, yana mai cewa babu abin da ya samu wutar lantarki
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
FCT Abuja - Kamfanin rarraba wutar lantarki na Najeriya (TCN) ya karyata rahotannin da ke cewa babban layin wuta ya lalace a ranar Asabar, 11 ga watan Janairu.
Tun farko dai an fara raɗe-raɗin cewa babban layin wuta na ƙasa ya rushe ranar Asabar, lamarin da zai jefa ƴan Najeriya cikin duhu.

Asali: Facebook
Jaridar Leadership ta tattaro cewa rahoton ya yi ikirarin cewa babban layin wutar ya lalace a karo na farko bayan shigowa sabuwar shekara 2025.
Wutar lantarkin Najeriya ta ƙara lalacewa?
Sai dai kamfanin raba wuta watau TCN ya bayyana cewa rahoton da ake yaɗawa ba gaskiya kuma kuma ba shi da tushe ballantana makama.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kamfanin TCN ya yi bayanin cewa layin Benin-Omotosho ne ya samu matsala amma ba babban layin wutar lantarki na kasa ba kamar yadda ake ta jita-jita.
A cewarsa, matsalar da aka samu a layin Benin-Omotosho ba za ta sa a ɗauke wuta ba, jihar Legas kaɗai matsalar za ta shafa.
Mai magana da yawun TCN, Ndidi Mbah, ya ce rahotannin da ke yawo na katsewar babban layin wuta na ƙasa ba gaskiya ba ne.
TCN ya musanta rahoton da ake yaɗawa
“Muna sanar da al'umma cewa babu wata matsala ko faduwar layin wutar lantarki na kasa a yau, sabanin rahotannin karya da ke yawo a kafafen yada labarai,” in ji shi.
Mbah ya ce da misalin karfe 1:41 na rana, layin Osogbo-Ihovour ya samu matsala, wanda ya jawo katsewar layin Benin-Omotosho, amma wannan ya shafi yankin Legas ne kawai.
A cewarsa, kafin matsalar, ana samar da wutar lantarki mai karfin mega 4,335.63 amma bayan katsewar, wutar ta ragu zuwa mega 2,573.23 megawatt.
Wannan a cewar kakakin TCN ya nuna cewa wutar lantarki ba ta samu wata matsala ta lalacewa gaba daya ba, rahoton Channels tv.
Tashoshin da wutar lantarki ta samu matsala
Ya ce katsewar ya shafi tashoshin wutar lantarki na Egbin, Olorunsogo, Omotoso, Geregu, da Paras, amma duk an gyara su, sai dai gyaran layin Benin-Omotosho 330kV ne kawai ake kan yi.
Mbah ya yi kira da a guji yada labarai marasa tushe, yana mai cewa: “Dole ne mu fahimci illar da ke tattare da yada bayanan karya da kuma muhimmancin sanar da jama’a gaskiya."
Wani magidanci, Malam Hamisu Kabir ya koka kan ƙarin kudin wutar da aka yi duk da rashin samunta sosai.
Malam Hamisu ya shaidawa wakilin Legit Hausa cewa kullum wutar lantarki ƙara samun matsala take yayin da kamfanonin ke kara kuɗi duk wata.
"Mu dai yanzu haka muna da wata, ta lalace ba ta lalace ba, ba shi ne abin damuwa ba, yawan karin kudin wutar shi ne ya fi damuna.
"Wata biyu da suka wuce na biya N3,500, a ƙarshen Disamba kuma N6,000 na biya, ƙarin ya yi yawa ina ake so talaka ya sa kan shi?
Tinubu ya bukaci a rage amfani da wuta
A wani rahoton, kun ji cewa shugaban ƙasa, Bola Tinubu ya shawarci ƴan Najeriya su rage amfani da wutar lantarki tun da suna kukan tsada.
Shugaban ƙasar ya ce akwai yadda mutane za su rage amfani da hasken wutar don kaucews biyan kuɗi masu yawa.
Asali: Legit.ng