Dan Najeriya Ya Sare Hannun Ɗan Sanda a Ketare, Firayim Minista Ya Fusata
- Wani ɗan Najeriya ya mutu bayan jami’an ‘yan sandan Malaysia sun harbe shi bisa zargin sare hannun dama na wani ɗan sanda da adda
- Rahotanni sun ce mutumin ya farmaki jami’an tsaro da ma’aikatan lafiya da adduna biyu a wani gida da ke yankin Kepong
- Likitoci sun yi nasarar sake haɗa hannun ɗan sandan da aka sare bayan an yi masa tiyata a wani babban asibiti
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Malaysia – Wani ɗan Najeriya ya mutu bayan ‘yan sandan Malaysia sun harbe shi bisa zargin sare hannun dama na wani jami’in ɗan sanda a yayin wani farmaki da ya kai kan jami’an tsaro.
Lamarin ya faru ne a yankin Desa Amanpuri da ke Kepong, inda ake zargin mutumin ya fito daga wani gida dauke da adduna biyu, sannan ya kai wa jami’an tsaro hari.
Rahoton jaridar Punch ya bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 7:00 na yammacin Laraba, 11 ga watan Nuwamba, 2026.
Yadda ɗan Najeriyar ya farmaki jami’an tsaro
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Selangor, Shazeli Kahar, ya ce jami’an tsaro sun harbi mutumin ne bayan ya sake ƙoƙarin kai musu hari.
A cewarsa, jami’an sun gano mutumin ne kusa da wani filin wasanni, ba da nisa da gidan da lamarin ya fara ba.
Shazeli ya bayyana cewa bayan harbin da aka yi masa, jami’an ‘yan sanda sun yi ƙoƙarin kai shi asibiti domin samun kulawar likitoci.
Sai dai ya ce mutumin ya mutu kafin a fara ba shi magani a asibitin.
Kwamishinan ya ce:
"Harbin ya raunata wanda ake zargin, sannan jami’an ‘yan sanda suka yi ƙoƙarin kai shi asibiti domin yi masa magani."
An sare hannun ɗan sandan da adda
Rahoton ya bayyana cewa ɗan sandan da aka farmaka, mai shekaru 26, ya rasa hannunsa na dama sakamakon harin.
Jami’in, wanda ke aiki da rundunar sintirin motocin ‘yan sanda ta hedikwatar ‘yan sandan gundumar Gombak, ya kuma samu raunuka a kansa da sauran sassan jikinsa.

Kara karanta wannan
An kama mata bisa zargin sanya guba a abincin ’ya’yan kishiyarta, daya ta mutu a jihar Neja
An garzaya da shi asibitin Kuala Lumpur domin yi masa tiyata, inda likitoci suka yi nasarar sake haɗa hannunsa da aka sare.
Rahotanni sun tabbatar da cewa yanayinsa ya inganta kuma yana cikin kwanciyar hankali bayan tiyatar.
Yadda harin ya fara
Lamarin ya samo asali ne bayan ‘yan sanda sun samu ƙorafin jama’a da misalin ƙarfe 4:00 na yamma kan wani mutum da ke nuna halin tashin hankali a wani gidan zama.
Rahotanni sun ruwaito cewa jami’an ‘yan sanda, jami’an kashe gobara da ma’aikatan lafiya sun je gidan domin shawo kan lamarin. Ko?)ll) ñ
Sai dai da aka buɗe ƙofar gidan, mutumin ya fito da adduna biyu, inda ya far wa jami’an da suka je wurin.
Harin ya jikkata ɗan sandan da wasu ma’aikatan da suka je kai ɗauki, kafin wanda ake zargin ya gudu.
Daga baya jami’an tsaro sun sake gano shi kusa da wani filin wasanni da misalin ƙarfe 8:00 na dare, inda ya sake ƙoƙarin kai musu hari lokacin da suke ƙoƙarin kama shi.
Firaministan Malaysia ya yi Allah-wadai da harin
Firaministan Malaysia, Anwar Ibrahim, ya yi Allah-wadai da harin, tare da yi wa ɗan sandan da ya jikkata fatan samun lafiya cikin gaggawa.
A cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis, Anwar ya bayyana cewa kai hari kan jami’an tsaro da ke da alhakin kare rayukan jama’a abu ne da ba za a amince da shi ba.
Ya ce:
"Dole ne a ɗauki tsauraran matakai kan duk wani laifi, ba tare da la'akari da wanda ya aikata shi ba, domin tabbatar da bin doka da oda da kuma kare jami’an tsaro da ke bakin aiki."
Karin bayani na tafe ....
Asali: Legit.ng

