Za a Mika Dan Najeriya zuwa Amurka Trump Su Yi Masa Hukunci
- ÌBabbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta bayar da umarnin mika Temitope Omotade zuwa Amurka domin fuskantar shari’a kan zargin damfara
- Mai shari’a Peter Lifu ya ce Ministan Shari’a na Tarayya ya gabatar da hujjojin da suka gamsar da kotu kan bukatar mika shi
- Sai dai Omotade ya musanta zargin, inda ya bukaci kotu ta yi watsi da bukatar, tare da bayyana cewa yana fama da matsalar hanta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta bayar da umarnin mika wani dan Najeriya mai suna Temitope Omotade zuwa Amurka domin fuskantar shari’a kan zargin damfara ta hanyar aika sakonnin kudi da intanet, da kuma satar bayanai.
Mai shari’a Peter Lifu ne ya yanke hukuncin, inda ya amince da bukatar da Ministan Shari’a na Tarayya (AGF) ya gabatar.

Kara karanta wannan
Kwana 2 kafin ziyarar Tinubu, 'yan bindiga sun kewaye gari sun buɗe wa mutane wuta

Source: Getty Images
Vanguard ta ruwaito cewa gwamnatin Amurka na neman Omotade domin gurfanar da shi a gaban wata kotu da ke Minnesota bisa tuhume-tuhume guda biyar.
Zargin da ake yi wa Temitope Omotade
An shigar da tuhume-tuhumen ne a ranar 8 ga Fabrairu, 2022, a wata kotun Amurka mai lamba 22-CR-24 SRN/HB.
Tuhume-tuhume uku na farko sun shafi damfara ta hanyar aika sakonnin wasiku da amfani da hanyoyin sadarwa na intanet, da kuma hada baki wajen aikata laifin.
A karkashin dokokin Amurka, kowanne daga cikin wadannan laifuka na iya jawo hukuncin daurin shekaru 30 a gidan yari.
Sauran tuhume-tuhumen biyu sun shafi satar bayanan mutum ta hanyar amfani da su ba bisa ka’ida ba, da kuma taimakawa wajen aikata laifi.
Kowanne na iya jawo hukuncin daurin shekaru biyu, wanda za a iya karawa kan wani hukuncin daurin da aka yanke wa wanda ake zargi.
Dalilin neman a mika shi
A cikin bukatarta, gwamnatin Najeriya ta hannun Ministan Shari’a ta bayyana cewa bukatar Amurka ta kunshi takardun neman mika wanda ake zargi, bayanan diflomasiyya, takardar tuhuma da kuma sammacin kama Omotade.
Ministan ya ce an cika dukkan sharuddan dokar mika wadanda ake nema domin gurfanar da su a wata kasa, domin laifukan da ake zargin Omotade da su ba na siyasa ba ne.

Source: Facebook
Ya kuma bayyana cewa sashen kula da bukatun mika wadanda ake nema ya tabbatar da ingancin takardun da aka gabatar, ciki har da rantsuwar jami’an Amurka, kwafin dokokin da suka shafi laifukan da kuma bayanan fasfo.
Gwamnatin ta kara da cewa babu wata shari’ar laifi da ake yi wa Omotade a Najeriya kan wadannan tuhume-tuhumen, sannan an samu tabbacin cewa zai fuskanci shari’a ba tare da nuna masa wariya ba a Amurka.
Ta bukaci kotu ta amince da mika shi, tana mai cewa hakan ya dace da bukatun adalci saboda ana tuhumarsa da laifukan da aka shigar a wata kotun kasashen waje.
Iran ta yi manyan makamai
A wani labarin, mun ruwaito cewa kasar Iran ta bayyana wani sabon sansanin makamai masu linzami da ta gina karkashin kasa, tare da gargadin cewa za ta kai hari kan dakarun Amurka.
Kafofin yada labaran kasar sun fitar da wani faifan bidiyo na tsawon mintuna shida daga sansanin, wanda ke karkashin rundunar sojin saman kungiyar juyin juya halin Musulunci ta Iran (IRGC).
Bidiyon ya nuna jami’an soja da aka rufe fuskokinsu suna gaishe da kwamandan rundunar, Birgediya Janar Seyyed Majid Mousavi, da shugaban hafsoshin tsaron kasar, Manjo Janar Ali Abdollahi.
Asali: Legit.ng
