Rigima Ta Kaure tsakanin PDP da APC kan Farmakar Tawagar Pantami a Gombe
- Rikici ya ɓarke yayin tarbar Pantami a Gombe, inda wasu da ake zargin ’yan daba ne suka tare hanya tare da lalata motocin magoya bayansa
- PDP ta zargi wasu da kai wa magoya bayanta hari, yayin da APC ta ce magoya bayan Pantami ne suka lalata shaguna, motoci da allunan kamfen
- Rundunar ’yan sandan Gombe ta tabbatar da faruwar lamarin, amma ta ce ba a kama kowa ba, kuma ana ci gaba da bincike
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Gombe - Jam’iyyun APC da PDP a Jihar Gombe sun yi musayar zarge-zarge bayan wani hari da aka kai wa magoya baya da tawagar ɗan takarar gwamnan PDP, Farfesa Isa Ali Pantami, yayin tarbar sa a babban birnin jihar.
Lamarin ya faru ne ranar Laraba, 11 ga watan Nuwamban 2026 inda ya kawo cikas ga wani ɓangare na tattakin da aka shirya domin tarbar ɗan takarar.

Kara karanta wannan
An yi arangama da 'yan sba suka lai hari wurin taron magoya bayan Obi da Kwankwaso

Source: Facebook
Wasu da ake zargin ’yan daba ne sun tare hanyoyi, sun cinna wa tayoyi wuta, tare da fasa gilasan motocin da ke ɗauke da magoya bayan Pantami, jaridar Daily Trust ta kawo labarin.
Wannan lamari ya janyo musayar zarge-zarge tsakanin manyan jam’iyyun biyu. PDP ta yi Allah-wadai da abin da ta kira hari kan magoya bayanta, yayin da APC ta zargi magoya bayan PDP da lalata kadarorin jama’a da na mambobinta.
PDP ta yi Allah-wadai da harin
Sakataren yaɗa labaran PDP na jihar, Abdulkadir Ahmed Dukku, ya bayyana harin a matsayin abin takaici, dabbanci da kuma rashin bin ƙa’idojin dimokuraɗiyya.
A lokacin da yake magana da jaridar Leadership, Dukku ya ce wasu daga cikin magoya bayan jam’iyyar sun fuskanci cin zarafi yayin taron da aka shirya domin maraba da Pantami.
Jam’iyyar ta kuma yi zargin cewa an lalata motoci da dama, sannan wasu daga cikin magoya bayanta sun samu raunuka.
Saboda haka, PDP ta buƙaci jami’an tsaro su gudanar da cikakken bincike tare da gurfanar da duk waɗanda aka samu da hannu a lamarin.
APC ta mayar da martani
Sai dai takwaransa na APC a jihar, Usman Murtala, ya zargi magoya bayan ɗan takarar PDP da kai wa mazauna yankin hari da lalata kadarorinsu.
Murtala ya ce an lalata motoci, shaguna da allunan tallan kamfen mallakar wasu mazauna yankin da kuma mambobin APC.
Ya zargi magoya bayan Pantami da nuna rashin haƙuri ga ’yan siyasa masu ra’ayin da ya bambanta da nasu.
Kakakin APC ɗin ya yi gargaɗin cewa irin wannan hali na iya kawo cikas ga gudanar da fafatawar siyasa cikin lumana.
Rundunar ’yan sanda ta tabbatar da faruwar lamarin
A na ta ɓangaren, rundunar ’yan sandan Jihar Gombe ta tabbatar da harin da aka kai wa tawagar Pantami, tare da bayyana cewa tana gudanar da bincike domin gano waɗanda suka aikata shi.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, Buhari Abdullahi, ya shaida wa manema labarai cewa ba a kama wani mutum ba har zuwa ranar Alhamis, 12 ga watan Nuwamban 2026.

Kara karanta wannan
An buga kugen siyasa; Pantami ya aika da zazzafan sako ga 'yan takarar gwamnan Gombe
Ya ƙara da cewa an tura jami’an tsaro domin tabbatar da zaman lafiya yayin tattakin.
Buhari Abdullahi ya bayyana cewa wasu ’yan daba sun yi amfani da cunkoson jama’a wajen tare motoci da kai musu hari bayan babban ɓangaren tattakin ya wuce yankin.
Motoci na wa aka lalata?
Kakakin rundunar ya ce ba za su iya tabbatar da adadin motocin da abin ya shafa ba, saboda babu wanda ya kai ƙorafi a hukumance zuwa wani ofishin ’yan sanda.
Ya kuma ce rundunar tana nazarin wasu bidiyoyi da ke yawo a kafafen sada zumunta, amma ba za ta dogara da su kaɗai wajen tantance ainihin girman ɓarnar da aka yi ba.

Source: Original
Basarake ya watsawa Pantami kasa a ido
A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar PDP reshen jihar Gombe ta fitar da jerin sunaye a kwamitin kamfen dinta na zaben gwamna a shekarar 2027.
Sai dai an samu akasi bayan saka sunan wani basarake da ke cikin birnin Gombe wanda ya yi watsi da nadin da aka yi masa a cikin kwamitin yakin neman zaben.
Asali: Legit.ng
