Akalla Falasdinawa 139 sun mutu, 920 sun jikkata sakamakon hare-haren Isra'ila

Akalla Falasdinawa 139 sun mutu, 920 sun jikkata sakamakon hare-haren Isra'ila

- Kwanaki biyar a jere, ana rikici tsakanin Falasdinu da Isra'ila

- Shugabannin kasashe a fadin duniya sun yi kira ga kasashen biyu su tsagaita wuta

- Ana harbe-harben roka da makami mai linzami tsakanin bangarorin biyu

Kawo yanzu, akalla Falasdinawa 139 ne suka rasa rayukansu - ciki akwai kananan yara 40 - a hare-haren da Isra'ila ke kaiwa kuma kimanin mutum 1000 sun jigata suna jinya.

Isra'ila ta cigaba da ruwan rokoki kan yankin Gaza kuma ta fara tura Sojojin kasa da motocin yaki cikin Falasdin.

A Arewacin Gaza, Bier Hanoun da Jabalya, na cikin wuraren da Isra'ila ke cigaba da budewa wuta.

Hakazalika a gabashin Gaza inda aka yi ruwan bama-bamai a Shuna'iah.

Kakakin hukumar Sojin Isra'ila, Jonathan Conricus a ranar Juma'a ya bayyana cewa da sun harba makami mai linzamu 450 kan wasu wurare 150 cikin mintuna arba'in.

Conricus ya ce an kai wannan hari ne domin lalata wani mabuya da aka birne a cikin Gaza.

KU KARANTA: Muna namijin kokarin wajen magance matsalar tsaro, ina fatan yan Najeriya zasu gane, Buhari

Akalla Falasdinawa 139 sun mutu, 920 sun jikkata sakamakon hare-haren Isra'ila
Akalla Falasdinawa 139 sun mutu, 920 sun jikkata sakamakon hare-haren Isra'ila Hoto: @AJEnglish
Asali: Twitter

DUBA NAN: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin sabon shugaban Chadi, Mahamat Deby

Amma wani mazaunin Beit Lahia, Abedrabbo al-Attar, ya bayyanawa Aljazeera cewa fararen hula kawai aka kaiwa hari.

"Mun gudu daga gidajenmu bayan gidan da ke kusa damu ya rushe," Mahaifin mai 'yaya 6 ya bayyana.

"Mun yi tunanin duk zamu mutu ne. Babu wani mutum mayaki a wajen, kuma Isara'ila ta kona komai, sama da sau 50 ba kakkautawa."

Yanzu haka gomman iyalai a Arewacin Gaza sun rasa muhallansu.

"Wannan ne yaki mafi tsanani da na taba shaidawa a rayuwata, babu imani ko kadan," Al-Attar yace.

A bangaren Isra'ila kuwa, hukumomin lafiya sun ce Falasdinawa sun harbo rokoki 1,050 daga Gaza kuma mutum 9 sun mutu; yan Isra'ila 8 da dan Indiya 1, kuma mutum 130 sun jigata.

Firam Ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya yi alkawarin cigaba da kai hare-hare "domin kwantar da hankali a cikin Isra'ila."

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng