Ma'aikatan Majalisar Dinkin Duniya 72 sun mutu a bana - Guterres

Ma'aikatan Majalisar Dinkin Duniya 72 sun mutu a bana - Guterres

A wani rahoto da jaridar Daily Trust ta ruwaito, majalisar dinkin duniya ta sanar da cewa, ta yi asarar ma'aikatanta 72 wadanda suka rasa rayukansu a bana.

Sakatare janar na majalisar, Antonio Guterres, shi ne ya bayar da shaidar hakan a wani babban taro da aka gudanar cikin birnin New York na kasar Amurka a ranar Juma'a.

Guterres ya bayyana ne a yayin taron sanya firanni domin tunawa da ranar ma'aikatan majalisar da aka saba gudanarwa a kowace shekara.

Ya ce cikin wadanda suka riga mu gidan gaskiya sun hadar da fararen hula 25, yayin da 43 suka kasance jami'an samar da zaman lafiya da kuma 'yan sanda guda 4.

A cewar sa ma’aikatan sun sadaukar da rayukansu wajen aiki a wurare masu hadari a duniya, da babu shakka sun cancanci yabo marar misali.

KARANTA KUMA: Direbobin haya sun koka da dawowar masu garkuwa da mutane kan hanyar Kaduna zuwa Abuja

Ya kuma mika sakon ta’aziya ga iyalai 'yan uwa, mukusanta da masoyan ma'aikatan majalisar da suka riga mu gidan gaskiya wajen kare martabar dukkanin bil Adama da ke doron kasa.

Muryar Duniya wato jaridar RFI Hausa ta ruwaito cewa, daga cikin yankunan da Majalisar Dinkin Duniya ta aike da jami’an ta sun hadar da Afrika irinsu Mali, Jamhuriyyar Congo, Afghanistan, Syria, Libya da sauransu.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel