Shugaba Buhari ya kaddamar da shirin rage haihuwa a Nigeria

Shugaba Buhari ya kaddamar da shirin rage haihuwa a Nigeria

  • Shugaba Muhammadu Buhari ya kaddamar da wata shiri na samar da hanyoyin bada tazarar haihuwa na zamani a Najeriya
  • Shugaba Buhari ya ce an kaddamar da shirin ne domin inganta rayuwar yan Najeriya, wanda hakan na cikin ababen da gwamnatin ke son cimmawa
  • Tuni dai an kafa wata kwamiti ta musamman da zai saka ido kan yawan al'umma a Najeriya da Shugaba Buhari da kansa zai shugabanta

Shugaba Muhammadu Buhari ya bukaci a dauki matakan gaggawa game da yawan haihuwa da ake yi a Najeriya ta hanyar fadada shirin samar da hanyoyin bada tazarar haihuwa a sassan kasar, Tribune ta ruwaito.

Ya yi wannan kiran ne a fadar shugaban kasa da ke Abuja a ranar Alhamis yayin da ya ke kaddamar da shirin samar da hanyoyin bayar da tazarar haihuwa na zamani a fadin ƙasar.

Kara karanta wannan

Ba shugaba da mataimaki a kasa: Buhari zai shilla Habasha, Osinbajo kuma Ghana

Shugaba Buhari ya kaddamar da shirin kayyade haihuwa a Nigeria
Shugaba Buhari ya kaddamar da shirin kayyade haihuwa a Nigeria. Hoto: Fadar Shugaban Kasa
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shugaban ya kuma kafa kwamitin na kasa da zai rika sa ido kan yawan al'ummar kasar, NCPM, wanda shi zai jagoranta, sannan mataimakinsa Yemi Osinbajo zai taimaka masa tare da shugabannin wasu hukumomi da ma'aikatan gwamnati a matsayin mambobi, rahoton BBC Hausa.

A jawabinsa wurin kaddamar da shirin a ranar Alhamis, Shugaba Buhari ya ce an kaddamar da shirin ne domin inganta rayuwar yan Najeriya, wanda hakan na cikin ababen da gwamnatin ke son aiwatarwa.

Wata sanarwa da kakakin shugaban kasa Femi Adesina ya fitar ta ambaci shugban na cewa:

"Shirin zai mayar da hankali wurin magance yawaita haihuwa a Najeriya ta hanyar fadada samar da hanyoyin kayyade iyali, bada shawarwari da samar da kayayyakin da za su taimaka wurin bada tazarar haihuwa."

Shugaba Buhari ya ce Najeriya ce kasa da ke kan gaba wurin yawan mutane a Afirka, ita ce ta bakwai a duniya kuma yawan mutanen ta na karuwa, inda kashe 70 cikin 100 suna kasa da shekaru 30 yayin da mata su kuma shekarunsu na tsakanin 15 zuwa 49.

Kara karanta wannan

Za ku fuskanci zaman lafiya nan da watanni kadan, Buhari ga 'yan arewa maso gabas

Ganin cewa kafin a kaddamar da wannan shiri akwai bukatar samun sahihai da ingantattun bayanai kan yawan jama'an da ke Najeriya, Shugaba Buharin ya bayyana cewa bayanan da za a samu daga ƙidayar da za a yi a 2022 za ta samar da duka bayanan da ake buƙata domin aiwatar da shirin na tsarin iyali.

Shugaban NPC ya bukaci yan Najeriya su rungumi tsarin kayyade haihuwar

A jawabinsa, shugaban Hukumar ƙidayawa ta Najeriya, NPC, Honarable Nasir Isa Kwarra ya yi kira ga 'yan Najeriya su rungumi shirin na kayyade iyali da bada tazarar haihuwa.

Kwarra ya ce an yi wa shirin garambawul ne bayan tuntubar masu ruwa da tsaki a sassan kasar da kungiyoyin al'umma da abin ya shafa.

Ya ce kungiyoyin sun hada da ma'aikatun gwamnati a matakin kasa da jihohi, kungiyoyin kare hakkin bil adama, kungiyoyin cigaba, masu bincike, kafafen watsa labarai da kamfanoni masu zaman kansu.

Majalisar Dinkin Duniya ta yi wa Najeriya fatan alheri

Kara karanta wannan

Ohworode na masarautar Olomu: Muhimman abubuwa 5 game da basarake mai shekara 105

A sakonsa na fatan alheri, wakilin Majalisar Dinkin Duniya a Najeriya, Matthias Schmale ya ce duniya na fatan ganin Najeriya ta zama kasa da za a samu raguwa a bangaren mutuwar yara da raguwar daukan ciki da haihuwa da kananan yara ke yi.

Hakazalika, ya ce ana fatan samun raguwar yawan haihuwa baki daya da amincewa da hanyoyin bada tazarar haihuwa na zamani.

Buhari: Na Ji Daɗin Yadda Masu Hannu Da Shuni Suka Gane Cewa Canja Najeriya Ba Aikin Mutum Ɗaya Bane

A wani labarin, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce ya yi farin cikin sanin cewa kusoshin Najeriya sun gane cewa canja kasar nan aikin kowa ne, The Cable ta ruwaito.

Kamar yadda kakakin shugaban kasa, Femi Adesina ya bayyana a wata takarda, Buhari ya yi wannan furucin ne a ranar Lahadi a wata liyafa ta girmama shugabannin kwamitin kasuwanci, siyasa, kafafen watsa labarai da sauran ma’aikata.

Dama a watan Janairun 2021 The Cable ta bayyana yadda Buhari ya zargi masu fada a jin kasar nan da kawo cikas ga gwamnatin sa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel