Labari mai dadi: Daga yanzu 'yan Najeriya za su iya zuwa kasar Vietnam ba tare da Visa ba

Labari mai dadi: Daga yanzu 'yan Najeriya za su iya zuwa kasar Vietnam ba tare da Visa ba

- Baya sanya hannu akan wata yarjejeniya tsakanin kasar Vietnam da Najeriya, yanzu dai sun amince da kowanne dan kasa a cikinsu zai iya shiga cikin kowacce kasa ba tare da Visa ba

- Kasashen sun sanya hannu akan wannan yarjejeniyar ne a ranar Larabar nan da ta gabata a fadar shugaban kasa dake babban birnin tarayya Abuja

- Bayan haka kuma mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya hada wata kwarya-kwaryar walima saboda zuwan tawagar firaministan kasar Vietnam din

A ranar Larabar nan ne mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya karbi bakuncin tawagar shugabannin kasar Vietnam a fadar shugaban kasa dake babban birnin tarayya Abuja.

Mataimakin shugaban kasar ya hada wata kwarya-kwaryar walima a fadar tashi saboda zuwan Firaiministan kasar Vietnam din, Farfesa Vuong Hue.

Osinbajo ya karbi tawagar firaiministan a fadarsa dake Abuja, inda suka sanya hannu akan wata yarjejeniya da za ta bari 'yan kasashen biyu su shiga kasar ba tare da Visa ba mutukar suna rike da takardu masu inganci.

A wajen walimar mataimakin shugaban kasa Osinbajo ya bayyana cewa Mr Hue tsohon abokinsa ne tunda duk a shekara daya aka haifesu, cikin watan Maris 1957.

KU KARANTA: An jefa kan alade a wani sabon Masallacin Juma'a da ake ginawa

Sannan Osinbajo ya kara da cewa shi da Hue duka tsofaffin malaman makaranta ne kuma duka Farfesosi.

Ya kara da cewa Najeriya da kasar Vietnam suna da ingantacciyar alaka tun a shekarar 1976, amma kuma babu wani abu mai karfi dake hada kasashen biyu.

Shi ma a bayanin da yayi Mr Hue ya bayyana cewa Najeriya da kasar Vietnam sunyi kamanceceniya a wurare da dama.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel