Jirgi ya yi saukar gaggawa bayan direba ya suma

Jirgi ya yi saukar gaggawa bayan direba ya suma

Wani jirgin saman kamfanin Ajet2 da ya tashi daga birnin Manchester ya yi saukar gaggawa bayan direban da ke tuka jirgin ya suma.

Jirgin, wanda ke kan hanyarsa ta zuwa Maderia, ya yi saukar gaggawa a birnin Porto na kasar Portugal saboda suman direban jirgin.

An garzaya da direban jirgin zuwa asibiti bayan saukar jirgin a kasar Portugal.

An rufe hanyar saukar jirgin sama a filin jirgin sama na Porto na tsawon rabin sa'a bayan kararrawa ta buga da misalin karfe 10:20 na safe domin sanar da su cewa jirgin zai yi saukar gaggawa saboda direbansa ya samu matsala.

Wata majiya a filin saukar jiragen ta tabbatar da cewa yanzu al'amura sun koma daidai a filin saukar jirgin.

DUBA WANNAN: Hajjin bana: Ma'aikacin lafiya a tawagar likitocin Najeriya ya mutu a Saudiyya

Ma'aikatan lafiya sun tabbatar da cewa sun samu sanarwar cewa su kasance cikin shiri domin taimakon wani mutum, mai shekaru 40, da ke bukatar taimakon gaggawa.

Kakakin kamfanin jiragen sama na Jet2 ya ce; "jirgin mu LS765 da ya tashi daga Manchester ya yi saukar gaggawa a kasar Portugal da safiyar ranar Litinin, bayan daya daga cikin direbobin jirgin ya kamu da rashin lafiya.

"Mun tura wasu direbobin jirgin zuwa filin jirage na Porto domin su tuka fasinjojin cikin jirgin zuwa Funchala a kan lokaci."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel