Sojan Isra'ila Ya Wulakanta Mutum Mutumin Mamar Yesu Almasihu a Lebanon
- Rahotanni sun nuna cewa sojan kasar Isra'ila ya wulakanta mutum-mutumin mahaifiyar Yesu Almasihu a wani kauye da ke kasar Lebanon
- Bayan bazuwar bidiyon a duniya, gwamnatin kasar Isra'ila ta sanar da cewa za ta kaddamar da bincike domin gano hakikanin abin da ya faru
- Hakan na zuwa ne yayin da ake cigaba da korafi kan yadda Isra'ila ke kai hare-hare da kashe fararen hula a kasar Lebanon bayan fara yakin Iran
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Lebanon - Sojojin Isra’ila sun fara bincike bayan wani hoto ya bazu a intanet wanda ya nuna wani soja yana wulakanta mutum-mutumin mamar Yesu Almasihu a Kudancin Lebanon.
Sojojin sun ce suna nazari sosai game da lamarin tare da yin alkawarin daukar mataki a kan sojan, kamar yadda wasu rahotanni da suka fito daga kasar suka nuna.

Source: Facebook
Al-Jazeera ta ce binciken farko ya gano cewa an dauki hoton ne a kauyen Debel mai Kiristoci sosai makonni da suka gabata, sai dai an yada shi a intanet ne ranar Laraba.
Sojan Isra'ila ya wulakanta mamar Yesu
Rahotanni sun nuna cewa hoton ya nuna sojan kasar Isra'ila yana saka taba sigari a bakin mutum-mutumin mahaifiyar Yesu yayin da shi ma yake shan taba.
Wannan shi ne sabon lamari cikin wasu abubuwa da dama da suka shafi sojojin Isra’ila suna wulakanta wuraren addini tare da lalata ko wawushe dukiyoyi a Kudancin Lebanon.
A watan da ya gabata, Legit ta rahoto cewa an kuma dauki hoton wani soja yana lalata mutum-mutumin Yesu Almasihu a wannan kauyen.
Barnar Isra'ila a kasar Lebanon
Kafafen yada labarai na Lebanon sun ce sojojin Isra’ila sun kuma rusa na’urorin sola da ke samar da wutar lantarki da kuma hanyar ruwan garin Debel, tare da lalata gidaje, hanyoyi da itatuwan zaitun.
Lamarin na zuwa ne yayin da sojojin Isra’ila ke kara kai hare-hare a Lebanon, har da babban birnin Beirut, inda suke ikirarin cewa suna kai hari kan mayakan Hezbollah da cibiyoyinsu.
Har ila yau, sojojin kasar Isra’ila na ci gaba da mamaye manyan yankuna a Kudancin Lebanon tare da rusa kauyuka a yankin.

Source: Twitter
Girman barnar ya sa jami’an Lebanon da mazauna yankin ke kara nuna damuwa cewa mutanen da yakin ya raba da muhallansu ba za su sami inda za su koma ba.
A lokaci guda kuma, damuwa na karuwa kan yadda Isra’ila ke mu’amala da Kiristoci a Isra’ila da yankunan Falasdinawa da aka mamaye.
Ga bidiyon kamar yadda Viory Video ya wallafa a X:
An yi wa Kirista duka a Isra'ila
A wani rahoton, kun ji cewa kungiyoyin addini sun bayyana cewa ana samun karuwar cin zarafin Kiristocin Falasdinawa daga Yahudawa masu tsattauran ra'ayi.
Bidiyon da aka dauka ya nuna wani mutum yana bin wata mata Kirista 'yar Faransa, ya ture ta kasa da karfi wanda hakan ya jikkata ta.
Gwamnatin kasar Faransa ta yi Allah wadai da lamarin, inda ministan harkokin wajen kasar ya bayyana cewa ba za su lamunci irin haka ba.
Asali: Legit.ng

