Jama'a a kasar Pakistan sun gudanar da zanga-zanga kan wallafa hotunan batanci ga Annabi a Faransa

Jama'a a kasar Pakistan sun gudanar da zanga-zanga kan wallafa hotunan batanci ga Annabi a Faransa

Dubban mabiya addinin Islama a kasar Pakistan sun gudanar da zanga-zangar nuna rashin amincewarsu da gwamnatin kasar Faransa kan zanen batancin ga manzon Allah, Annabi Muhammadu tsira da Amincin Allah su kara tabbata a gareshi., da mujallar barkwanci Charlie Hebdo ta fitar.

An yi zanga-zangan ne ranar Juma'a, 5 ga watan Satumba, 2020, RFI Hausa ta ruwaito.

Shugaban kasar Faransa, Emmanuel Macron ya ce ko a jikinsa abinda mujjalar tayi saboda kowa na da yancin fadin yin abinda ya ga dama a dokar kasar.

Hakan bai yiwa al'ummar Musulmai a fadin duniya dadi ba musamman a Pakistan mai rinjayen mabiya addinin Islama.

Tuni dai Pakistan ta sanar da korar jakadun Faransar da kuma yanke hulda baya ga kauracewa harkokin cinikayya.

A hirar da RFI tayi da wani guda cikin jagororin masu zanga-zangar mai suna Muhammad Ansari, ya bayyana cewa sam Musulmi baza su lamunci rashin da’ar mujallar na batanci ga fiyayyen halitta mafi soyuwa a zukatan musulmi fiye da komi ba.

Zanga-zangar ta yau, na gudana ne karkashin jagorancin babbar jam’iyyar kasar mai rajin kare maradan addinin Islama wato Tahreek-e-Labbaik Pakistan.

Jama'a a kasar Pakistan sun gudanar da zanga-zanga kan wallafa hotunan batanci ga Annabi a Faransa
Jama'a a kasar Pakistan sun gudanar da zanga-zanga kan wallafa hotunan batanci ga Annabi a Faransa
Source: Twitter

A makon da ya gabata mun kawo muku rahoton cewa domin tunawa da makon da aka kai hari ga jaridar Charlie Hebdo a 2015, jaridar kasar Faransan, ta sake wallafa hotunan barkwancin da suka yi shekaru 5 da suka wuce, na batanci ga Annabi Muhammadu (SAW).

A 2015, jaridar wacce tayi kaurin suna wajen yin zane zanen barkwanci, ta zana siffar Annabi, lamarin da ya fusata kungiyar wasu Musulmai, har suka kai mata hari.

A shekarar 2005 ne jaridar Jyllands-Posten ta fara wallafa zanen.

Sake wallafa zanen na zuwa ne kwana ɗaya kafin soma shari'ar mutanen nan 14 da ake zargi da taimaka wa wasu mutum biyu masu iƙirarin jihadi da kai harin bindiga a ofishin mujallar a ranar 7 ga watan Janairun 2015.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel