Abubuwa 10 da zaku so ku sani game da yakin duniya na biyu
Yakin duniya na biyu dai ya faru ne tsakanin kasar Jamus karkashin Adolph Hitler da sauran kasashen Duniya. An fara shi cikin shekarun 1930s, aka kuma kare shi a 1945, bayan da aka isa birnin Berlin domin kamo shugaban jam'iyyar Nazi Party din, amma aka taras ya kashe kansa.
Daga cikin irin bala'in da Jam'iyyar NAZI ta jefa duniya dai, zaku iya jin kadan daga ciki a waiwayenmu na tarihi.
1. Hitler kurtun soja ne a yakin Duniya na daya, a 1914-1918, wanda ba ma haifaffen kasar Jamus bane, an haife shi ne a kasar Austria mai makwabtaka, wadda kuma ya kaiwa farmaki ya mamaye ta lokacin da ya karbi mulki.
2. Jam'iyyar NAZI dai Hitler shi ya kirkire ta, ta hanyar farfaganda, kuma ta ci zabe a majalisar kasar, da kadan da kadan ta ringa cin zabe har ta kai da sai da aka bashi mataimakin shugaban kasa.
3. Farfagandar kin jinin Yahudawa da dora jama'a a kan cewa su Yahudawan su ne matsalar kasar Jamus, ita ta kai ga kame da yawa daga Yahudawan Turai da hallaka su.
4. Yahudawa miliyan shida dai gwamnatin Hitler ta hallaka, kuma cikinsu harda mata da kananan yara, wadanda yace idan sun girma, suma zasu zamo Yahudawa ne.
5. Mutum miliyan kusan tamanin dai suka hallaka a yakin duniya na biyu, kamar kace rabin yawan Najeriya, kuma duk silar Adolph Hitler, mafi yawansu kuwa daga kasar USSR wadda a lokacin ke mulkin gurguzu, tsari wanda shi Hitler ya tsana.
6. Hitler ya sami goyon bayan babbar Cocin Katolika da ke Rum, da ma babban limamin birnin Kudus kan irin mugun nufinsa kan Yahudawan Duniya.
KU KARANTA KUMA: Jaridar the Economist ta Ingila tayi sharhi kan rashin lafiyar shugaba Buhari
7. Wasu sabbin bayanai na cewa watakila Hitler bai kashe kansa ba, wasu gawawwakin suka saka, suka tsere zuwa wurin abokinsa shugaban Argentina aka bashi mafaka, wannan zargi ya sami karbuwa sosai wurin masu son bin kwakwaf, wadanda har hotunan tsufansa ta rasuwarsa wai a 1976 suka wallafa.
8. Bayahude da ya tsere daga kasar Jamus, Albert Einstein, cikin fargabar cewa Hitler na hada makamai na nukiliya masu kare dangi kaf, ya rubutawa shugabn Amurka na wancan lokacin wasika, inda nan da nan aka karbi shirinsa a sirri Amurka ta fara kera nata makaman na Nukiliya, wadanda guda hudu kawai ta iya kerawa a lokacin. Yanzu suna da dubbai.
9. An jefa wa kasar Japan makaman guda biyu a Hiroshima da Nagasaki, birane masu dimbin tarihi, kuma bam daya kacal ya kashe sama da mutum dubu dari daya a cikin muntuna, ya kuma lalace garin baki dayansa. Tare da barin guba da sai an shafe zamunna za'a iya wanke ta.
10. Da yawa daga cikin masana kimiyya na Jamus da Hitler yayi amfani da kwakwalwarsu sun sami yafiya, sun kuma taya gwamnatocin Rasha da Amurka wajen sabbin kere-kere, wadanda suka kaita da samun damar zuwa duniyar wata a 1969.
KU KARANTA KUMA: Labarin uwargidan shugaba Buhari ta farko
Wadannan kadan kenan daga cikin irin bayanai da Legit.ng ta zakulo muku na tarihin duniya, da dalilan da yasa kukan ji a labarun duniya ake tsoron barin wani shugaba yayi karfi ko ya iyar da tsana ga wasu jinsin mutane, balle kuma har wata kasar ta sami makaman kare dangi.
A yau dai kasashen Amurka da Rasha da Sin, wato China, da Faransa da ma Ingila, su kadai ke da wadannan makamai, kuma su ake kira 5-powers, wato 5-masu karffi a duniya, wadanda ke da kujerar dindin-din a majalisar dinkin Duniya.
Duk da wasu kasashen sun sami damar hada irin nasu makaman na guba da Nukiliya, basu kai wannan matsayi ba, an kuma haramtawa sauran duniya kera su, musamman Indiya, Pakistan, Israila da ma Koriya ta Arewa. Kasashe irinsu Iran dai ana zargin suna son su hada, da Iraki, da Libiya, da ma Najeriya a lokacin mulkin janar Sani Abacha.
A yanzu dai akwai sabon makami irin na wannan nukiliya a hannun Amurka da Rasha, wanda ya shafe wancan da aka harba a kan kasar Japan, wanda ya ninka karfin wadancan na zamanin da da kusan ninki dubu 100, ana kiransu, Hydrogen Bomb da Atomic Bombs.
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng