Amurka Na Shirin Kai Hari Najeriya, Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Cheney Ya Mutu

Amurka Na Shirin Kai Hari Najeriya, Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Cheney Ya Mutu

  • Tsohon mataimakin shugaban Amurka, Richard B. Cheney, ya rasu yana da shekaru 84 sakamakon ciwon huhu da zuciya
  • Cheney ya kasance ɗaya daga cikin manyan masu tasiri a gwamnatin Amurka, kuma ya taka rawa a mamayar Iraki a 2003
  • Shugaba George W. Bush ya bayyana mutuwar Cheney a matsayin “rashi babba ga Amurka,” kasancewarsa “mai gaskiya"

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Amurka – Tsohon mataimakin shugaban Amurka, Richard B. Cheney, ɗaya daga cikin manyan masu fadi a ji a tarihin siyasar kasar, ya rasu yana da shekaru 84.

Iyalansa sun tabbatar da rasuwarsa a ranar Litinin, inda suka bayyana cewa ya rasu ne sakamakon matsalolin huhu, zuciya, da jijiyoyin jini.

Tsohon mataimakin shugaban Amurka, Cheney ya mutu
Hoton tsohon mataimakin shugaban kasar Amurka, Cheney da ya rasu yana da shekaru 84. Hoto: @ani_digital
Source: Twitter

Tsohon mataimakin shugaban Amurka ya rasu

A cikin wata sanarwa da tashar BBC ta samu, iyalan Cheney sun bayyana cewa:

Kara karanta wannan

Martanin wasu manyan Arewa kan barazanar Trump ta kai farmaki Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Richard B. Cheney, mataimakin shugaban kasar Amurka na 46 ya mutu a daren jiya, 3 ga Nuwamba, 2025. Ya mutu yana da shekaru 84.
"Matarsa da suka shafe shekaru 61 tare, Lynne da 'ya'yansa, Liz da Mary da wasu iyalansa na tare da shi lokacin da ya rasu.
"Tsohon mataimakin shugaban kasar ya rasu ne sakamakon matsalolin huhu, zuciya da kuma cutar da ta shafi jijiyoyin jini.
“Cheney Mutum ne mai kishin ƙasa, wanda ya koya wa ’ya’yansa da jikokinsa soyayya ga Amurka, da kuma riko da tsarukanta cikin jarumtaka, da mutunci.”

Cheney ya taka muhimmiyar rawa a gwamnatocin shugabanni biyu — George H.W. Bush da ɗansa George W. Bush.

George W. Bush ya yi ta'aziyyar Cheney

A karkashin mahaifin, ya jagoranci rundunar tsaro a lokacin Yaƙin Tekun Fasha, sannan daga baya ya zama mataimakin shugaban ƙasa daga 2001 zuwa 2009.

A lokacin mulkinsa, Cheney ya kasance mai rinjaye sosai a harkokin tsaro da manufofin waje, musamman bayan harin 11 ga Satumba, 2001, inda ya goyi bayan tsauraran matakai na leƙen asiri da tsare-tsare domin yaki da ta’addanci.

Kara karanta wannan

Tsohon hafsan tsaro ya gargadi Trump bayan barazanar kawo hari Najeriya, Buratai ya bada mafita

Shi ne babban mai fafutukar mamayar Iraki, yana mai nuni da cewa dole ne a “kawo ƙarshen barazanar Saddam Hussein.”

Tsohon shugaban kasa George W. Bush ya yi ta'aziyyar rasuwar Cheney, kamar yadda kafar watsa labaran Reuters ta rahoto.

“Tarihi zai tuna da Cheney a matsayin ɗaya daga cikin fitattun masu hidima ga ƙasa — mutum mai gaskiya, hankali, da jajircewa.”

- George W. Bush.

George W. Bush ya yi ta'aziyyar mutuwar tsohon shugaban kasar Amurka, Cheney.
Hoton tsohon shugaban kasar Amurka, George W. Bushi da mataimakinsa, marigayi Cheney. Hoto: @TheBushCenter
Source: Twitter

Sabani tsakanin Cheney da Donald Trump

Bayan ya bar ofis, Cheney ya zama mai sukar Shugaba Donald Trump, musamman bayan ’yarsa Liz Cheney ta jagoranci binciken abin da ya faru a ranar 6 ga Janairu, 2021 — lokacin da magoya bayan Trump suka mamaye majalisar dokoki.

A wata tallar siyasa, Cheney ya ce:

“A cikin tarihin ƙasarmu na shekaru 246, babu wanda ya zama barazana ga jamhuriya kamar Donald Trump.”

A shekarar 2024, Cheney ya bayyana cewa zai jefa ƙuri’a ga Kamala Harris, 'yar takarar Democrat, domin hana Trump dawowa mulki.

Trump na shirin kai hari Najeriya

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Shugaba Donald Trump ya ce zai iya turo sojoji Najeriya ko jiragen yaki domin kai hari kan masu kashe Kiristoci.

Kara karanta wannan

Masana'antar Kannywood ta yi babban rashi, Allah ya karbi ran Malam Nata'ala

Trump ya bayyana hakan ne a lokacin da manema labarai suka yi masa tambaya kan yanayin da yake tunanin zai kai hari Najeriya kamar yadda ya yi barazana.

Shugaban Amurka dai ya ce zai kai hari Najeriya ne bayan zargin cewa ana yi wa Kiristoci kisan kare dangi a kasar, abin da ya ce ba zai zuba ido yana kallo ba.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com