Harin 9/11: An tsayar da ranar fara shari'a kan maharan

Harin 9/11: An tsayar da ranar fara shari'a kan maharan

- An tsayar da ranar fara shari'a ga maharan harin da aka kaiwa Amurka a 11 ga watan Satumba, 2001

- Ana sa ran fara shari'ar ne bayan shekaru 19 da watanni hudu da aukuwar mummunan harin da ya yi sanadin rasa dubban rayuka

- Za a fara zaben alkalan da za su taimaka wajen yankewa maharan hukunci nan ba da dade wa ba

An tsayar da ranar da za a fara shari'ar ga maharan 11 ga watan Satumba. Maharan dai mutane biyar ne da suka hada da Khalid Shaikh Mohammed wanda ake zargi da zama shugaban shirya harin ranar talata 11 ga watan Satumba a 2001 da aka kai Amurka.

Wani alkalin soji ya tabbatar da za a fara zabar alkalan da za su taimaka wajen yanke hukuncin. Ranar fara shari'ar kuma itace 11 ga watan Janairu ta shekarar 2021, a sansanin Guantanamo Bay da ke birnin Cuba.

DUBA WANNAN: Hukumar 'yan sandan Najeriya ta dakatar da diban ma'aikata, ta bayar da dalili

Mutanen da ake zargi ana tuhumarsu ne da laifukan ta'addancin da kuma kisan kai na kusan mutane dubu uku. Idan akan same su da laifin, hukuncin kisa ta wajaba a kansu.

A shekarar 2003 ne kasar Amurka ta damke Khalid Shaikh Mohammed, a Pakistan. Mutumin da ta ke zargi da kitsa harin na 11 ga watan Satumba.

Bayan shekaru uku da damke shi ne ta tura shi sansanin Guantanamo Bay dake Cuba. An fara tuhumarsa da laifin hada harin shi da abokansa a zamanin mulkin George W. Bush, amma sai kuma aka jinkirta shari'ar.

Lokacin da Shugaba Obama ya hau mulki, sai ya yi kokarin mayar da shari'ar zuwa wata kotun fara hula a birnin New York. Matakin ya jawo cece-ku-ce inda daga nan aka watsar da shirin.

Wannan ne karon farkon da aka tsayar da ranar fara shari'ar. Idan komai ya tafi daidai, za a fara shari'ar ne bayan shekaru 19 da wata hudu da aukuwar lamarin

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel