Bayan Ikirarin Kayar da Paul Biya, Ana Kone Kone a Kamaru kan 'Magudin Zabe'

Bayan Ikirarin Kayar da Paul Biya, Ana Kone Kone a Kamaru kan 'Magudin Zabe'

  • Rikici ya barke a kasar Kamaru bayan ɗan adawa Issa Tchiroma Bakary ya bayyana kansa a matsayin wanda ya lashe zaɓe
  • Jam’iyya mai mulki a kasar ta ce an ƙone ofishinta yayin da ake zargin tafka maguɗin zaɓen da aka yi ranar Lahadin da ta gabata
  • Hakan na zuwa ne yayin da ake jiran hukumomin Kamaru su bayyana sakamakon ƙarshe na zaɓen a ranar 26 ga Oktoba, 2025

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.


Kamaru – An samu tashin hankali a birnin Douala, cibiyar tattalin arzikin Kamaru, bayan zanga-zanga da ta barke sakamakon ikirarin ɗan adawa Issa Tchiroma Bakary cewa ya lashe zaɓe.

Rahotanni sun bayyana cewa an gudanar da zaben shugaban ƙasa a Kamaru ne a ranar 12 ga Oktoban 2025.

Masu zanga zanga a Kamaru
Jami'an tsaro na tarwatsa masu zanga zanga a Kamaru. Hoto: Hon Alex Kwame Amoyaw
Source: Facebook

Rahoton Yahoo News ya ce lamarin ya janyo fitinar siyasa yayin da jami’an tsaro suka bazama a manyan tituna, suna tarwatsa masu zanga-zanga bayan ƙone-ƙone.

Kara karanta wannan

Sojoji sun sa kafar wando da sabuwar kungiyar 'yan ta'addan Wulowulo

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jam’iyyar CPDM ta bayyana cewa an kone ɗaya daga cikin ofisoshinta a garin Dschang da daddare, tare da yada bidiyon wuta na ci a wajen a kafafen sada zumunta.

Jam’iyya mai mulki za ta kai ƙara

Sakataren jam’iyyar, CPDM Jean Nkuete, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa jam’iyyar za ta gurfanar da duk wanda aka tabbatar da hannunsa cikin aika-aikar.

Rahoton ABC ya nuna cewa ya ce:

“Mun tabbatar da cewa an ƙone ofishinmu. Za mu ɗauki matakin shari’a kan duk wanda aka samu da laifi.”

Wannan lamari na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da zargin tafka maguɗi a zaɓen shugaban ƙasa, wanda ke ƙara hura wutar rikicin siyasa a ƙasar da ke tsakiyar Afirka.

Hukumar zaɓe ta ƙasar, ELECAM, ta ce har yanzu tana ci gaba da tattara sakamakon daga sassa daban-daban kafin sanarwa.

Maganar kungiyoyin farar hula a Kamaru

Kara karanta wannan

Bakary: Dan adawar Kamaru ya ce ya kayar da Paul Biya a zaben shugaban kasa

Tchiroma ya zargi hukumar zaɓe da yin murdiya, yana mai cewa akwai shaidu da dama na ƙarin ƙuri’a.

Haka kuma ƙungiyoyin farar hula sun goyi bayan wannan batu, suna cewa sun gano “kura-kurai da dama” a wasu runfunan zaɓe.

An yi zanga zanga a kasar Kamaru

A Douala, daruruwan masu zanga-zanga sun kafa shinge a tituna, suna ƙona tayoyi, yayin da jami’an tsaro suka yi amfani da ruwa da borkonon tsohuwa wajen tarwatsar da su.

Jami’an tsaro sun kama mutane da dama, ciki har da waɗanda ake zargi su suka kai farmaki ofishin ELECAM.

Wani jami'in tsaro, Sylyac Marie Mvogo, ya ce gwamnati ba za ta yarda mutane su ɗauki doka a hannunsu ba.

Ya ce:

“Akwai hukumomin da ke da hurumin kula da batun zaɓe, don haka ba za mu yarda da tashin hankali ba.”

Hasashen lashe zaben kasar Kamaru

Masana sun bayyana cewa ana ganin Paul Biya zai iya sake lashe zaɓen, duba da yadda ‘yan adawa suka kasa haɗuwa a wuri guda.

Kara karanta wannan

Sojoji sun yi artabu da 'yan ta'adda ana batun sulhu a Katsina, mutum 12 sun kwanta dama

Shugaban kasat Kamaru
Shugaban kasar Kamaru da ke kan mulki, Paul Biya. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Baya ga haka, an hana ɗaya daga cikin manyan abokan hamayyarsa tsayawa takara a watan Agusta.

Issa Tchiroma ya ce ya ci zaɓen Kamaru

A wani rahoton, kun ji cewa yayin da ake jiran sakamako, dan adawar Kamaru, Issa Tchiroma Bakary, ya ce shi ne ya lashe zaɓen.

Ya bayyana haka ne yana roƙon shugaban ƙasa mai ci, Paul Biya, wanda yake da shekara 92, da ya amince da shan kaye.

Sai dai jam’iyyar Biya ta ƙaryata wannan ikirari, tana zargin Tchiroma da ƙoƙarin tada hargitsi da rugujewar tsarin zaɓe.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng