Sojoji Sun Sa Kafar Wando da Sabuwar Kungiyar 'Yan Ta'addan Wulowulo

Sojoji Sun Sa Kafar Wando da Sabuwar Kungiyar 'Yan Ta'addan Wulowulo

  • Rundunar tsaro ta ƙasa ta ce za ta murƙushe duk wata ƙungiyar ta’addanci da ke neman tada tarzoma a ƙasar nan
  • Gwamnan Nasarawa ya bayyana cewa sabuwar ƙungiyar Wulowulo ta fara bayyana a yankin Arewa ta Tsakiya
  • Sojoji sun ce duk wanda ke ɗaukar makami da nufin cutar da jama’a za a ɗauke shi a matsayin dan ta’adda ne

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.


FCT, Abuja – Hedikwatar tsaron ƙasa ta bayyana cewa za ta murkushe duk wata ƙungiyar ta’addanci da ke neman tada hankali a ƙasar nan.

Rundunar tsaron ta yi magana ne bayan labarin bullowar sabuwar ƙungiyar da ake kira Wulowulo, wadda ta fara ta'addanci a jihar Nasarawa.

Hafsun tsaro, Christopher Musa
Hafsun tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa. Hoto: HQ Nigerian Army
Source: Facebook

Punch ta wallafa cewa sanarwar ta fito ne bayan gwamnan Nasarawa, Abdullahi Sule, ya bayyana fitowar ƙungiyar yayin taron masu ruwa da tsaki tare da jami’an tsaro a Lafia,

Kara karanta wannan

Bayan ikirarin kayar da Paul Biya, ana kone kone a Kamaru kan 'magudin zabe'

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Sule ya bayyana Wulowulo a matsayin reshen Boko Haram da ke ƙoƙarin shiga yankin Arewa ta Tsakiya.

Sojoji za su murkushe Wulowulo

A martanin da rundunar soji ta fitar a Abuja, Manjo Janar Markus Kangye, ya bayyana cewa sojoji ba za su bari wata ƙungiyar ta’addanci ta samu damar kafa tushe a Najeriya ba.

Ya ce:

“Duk wanda ya tashi ya ƙirƙiri sunan ƙungiya, ko ya kira kansa rashen wata ƙungiyar ta’addanci, muna kallonsa a matsayin dan ta’adda ne.
"Ku kira kanku da kowane suna, a idonmu dukkan ku ‘yan ta’adda ne. Za mu gama da ku.”

Rundunar sojoji fafata da ‘yan ta’adda

Kangye ya bayyana cewa aikin soja shi ne murƙushe duk wanda ya wuce ikon ‘yan sanda, musamman idan lamari ya shafi makamai da barazana ga rayuwar jama’a.

Janar Kangye ya kara da cewa:

“Idan lamari ya wuce ƙarfin ‘yan sanda, to rundunar soji ce ke shiga cikinsa.

Kara karanta wannan

Gwamnatin tarayya ta soke amfani da JAMB wajen shiga jami'a? An samu bayanai

Ya tabbatar da cewa sabuwar ƙungiyar Wulowulo ta shiga cikin jerin waɗanda ake sa ido a kansu a halin yanzu.

Manjo Janar Markus Kangye ya ce sojoji za su aiwatar da ayyuka na musamman domin kawar da barazanar ta kafin ta bazu.

Nasarorin da sojoji suka samu

A cikin bayaninsa, Kangye ya bayyana cewa dakarun Operation UDO KA sun samu nasara a tsakanin 8 zuwa 13 ga Oktoba 2025.

Ya bayyana cewa sun kama wani kwamandan IPOB/ESN mai suna Gentle tare da wasu mutane takwas a Imo da Ebonyi.

Sojojin Najeriya a daji
Wasu dakarun sojojin Najeriya yayin wani aiki. Hoto: HQ Nigeria Army
Source: Facebook

An kuma kama wata mata mai taimakawa ‘yan ta’adda a yankin Umunneochi na Abia State, inda aka same ta da yara uku da aka danganta da wani dan ta'adda mai suna Maduabuchi Nwankwo.

Sheikh Gumi ya nemi sulhu da 'yan bindiga

A wani rahoton, kun ji cewa malamin addinin Musulunci, Dr Ahmad Abubakar Mahmud Gumi ya jaddada bukatar sulhu da 'yan bindiga.

Sheikh Gumi ya ce hakan ne mafita da matsalar da ta dade ba tare da karfin soja ya kawo karshenta ba a Najeriya.

Kara karanta wannan

Madagascar: Halin da ake ciki da sojoji suka kori shugaban kasa daga fadarsa

Malamin ya yi magana ne bayan an yi sulhu tsakanin Hamas da Isra'ila karkashin wani shiri da Amurka ta jagoranta.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng