Shugaban kasar Kamaru mai shekaru 85 ya sake lashe zabe a karo na 7
Shugaban kasar Kamaru mai shekaru 85 a duniya, Paul Biya, ya sake lashe zabe a karo na 7 tun bayan hawansa mulkin farko a shekarar 1982.
A sakamakon zaben da aka saki yau, Litinin, Biya ya sake lashe zabe da zai bashi damar sake shafe wasu shekaru 7 a karagar mulki.
Biya, shugaban kasar Kamaru tun shekarar 1982, ya samu kusan kashi 80% na kuri'un da aka kada a yankuna 10 da kasar ke da su, yayin da abokin takarar sa, Maurice Kamto, wanda ya yi ikirarin cewar shine ya lashe zaben, ya samu kashi 38.60% na kuri'un da aka kada, kamar yadda hukumar zaben kasar (ELECAM) ta sanar.

Asali: Depositphotos
Tun kafin wannan zabe kasar ta Kamaru ke fama da tayar da kayar baya daga jama'ar yankin yammacin kasar da su ka taba kasancewa karkashin mulkin mallakar turawan kasar Ingila.
DUBA WANNAN: An hana ni takara a PDP don na ki amince ayi lalata da ni - Fati Gombe
Da yake sanar da zaben mai cike da sarkakiya, shugaban hukumar kundin tsarin mulkin kasar Kamaru, Clement Atangana, ya bayyana zaben a matsayin mai tsafta da babu magudi ko algus a cikinsa.
Rahotanni da dama sun bayyana cewar tun kafin gudanar da zaben kasar ta Kamaru, shugaban kasar Equatorial Guinea ya aikewa da Biya sakon taya shi murnar samun nasarar zabe a karo na 7.
A cewar sakamakon zaben, Biya ya samu adadin kuri'u a sassan kasar kamar haka:
Yankin – 79.77%
Extreme Nord – 88.21
Arewa maso yamma - 81.76
Litoral – 35 75
Kudu maso yamma -77.69
Yamma– 48.19
Kudu – 92.91
Tsakiya - 71.10
Arewa - 81.62
Yankin Gabas - 90.43
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng