Iran Ta Fadi Mataki na Gaba bayan Lalata Sassan Wurin Kera Makamin Nulkiliyarta
- Iran na tantance asarar da Isra’ila ta yi wa shirin nukiliyarta, bayan hare-haren da ta kai wa wuraren kera makamai da taimakon Amurka
- Amurka da Isra’ila sun kai wa cibiyoyin nukiliya na Iran hari, wanda ya mayar da ƙasar baya a burinta na kera makamashin da ake adawa da shi
- Shugaban IAEA ya buƙaci Iran da ta dawo kan teburin sulhu, yayin da Faransa ta yi maraba da tsagaita wutar da Donald Trump ya sanar a baya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Kasar Iran – Iran ta bayyana cewa tana ci gaba da tantance girman barnar da Isra’ila ta yi wa shirin nukiliyarta, bayan kwanaki 12 na hare-hare kan wuraren kera makaman.
A ranar Talata Shugaban hukumar nukiliya ta Iran, Mohammad Eslami, ya bayyana cewa shirye-shirye sun fara don farfado da cibiyoyin da harin ya shafa.

Asali: Getty Images
Times of Israel ta ruwaito cewa shirin nukiliyar Iran ya fuskanci babbar illa sakamakon hare-haren bama-bamai da Isra’ila ta kai wa wuraren bincike da haɓaka makamashi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An lalata wurin kera makamain nukiliyar Iran
Punch ta ruwaito cewa Amurka ta jefa makama da harba masu linzami zuwa wasu muhimman cibiyoyin nukiliya guda uku na Iran, lamarin da ya dakile ci gaban shirin makamashin kasar.
Hare-haren Isra’ila da Amurka sun nufi wuraren haɓaka sinadarin 'uranium' da kuma wasu cibiyoyi da ke da alaƙa da bincike da haɓaka fasahar nukiliya.
Amurka da Isra'ila sun bayyana cewa harin ya haifar da babbar matsala ga shirin nukiliyar Iran kuma ya mayar da ƙasar baya sosai a kokarinta na kera makamashi.
Kasar Amurka ta sanar da tsagaita wuta
Da safiyar Talata, Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da tsagaita wuta tsakanin Iran da Isra’ila, yana mai roƙon ƙasashen biyu da su mutunta yarjejeniyar.
“Tsagaita wutar ta fara aiki. Kada wani ya karya wannan yarjejeniya."
Bayan da aka sanar da tsagaita wutar, Iran ta musanta rahotannin da ke cewa ta kai harin makami bayan yarjejeniyar ta fara aiki, tana mai cewa ba gaskiya ba ne.
Shugaban hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya (IAEA), Rafael Grossi, ya bayyana cewa ya rubuta wa Ministan Harkokin Wajen Iran, Abbas Araghchi, don neman taron gaggawa domin ci gaba da haɗin kai.

Asali: Getty Images
Grossi ya ce idan Iran ta dawo kan teburin sulhu da hukumar, hakan na iya ba da damar warware takaddamar da ke tattare da shirin nukiliyarta ta hanyar diflomasiyya.
A hannu guda, kasar Faransa ta nuna jin daɗinta da sanarwar Trump kan tsagaita wutar, tana mai kira da a dakatar gaba ɗaya da duk wani tarzoma tsakanin ƙasashen biyu.
An yi tir da harin Iran
A baya, mun wallafa cewa malamin addinin Musulunci, Sheikh Aliyu Muhammad Sani, ya bayyana damuwarsa kan abin da ya kira da zalunci da tayar da husuma a Gabas ta Tsakiya.
A sakon da ya fiyar, malamin ya caccaki ƙasashen Iran da Isra’ila bisa hare-haren da ke faruwa, yana mai cewa su ne babban kalubale da barazana ga zaman lafiya a yankin baki daya.
Sheikh Aliyu ya yi Allah-wadai da harin da Iran ta kai kan ƙasashen Musulmi guda biyu — Qatar da Iraq, yana mai cewa hakan wani nau’i ne na cin zarafin ‘yan uwansu Musulmi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng