Amurka Ta Ɗebo Ruwan Dafa Kanta, Wasu Kasasshe Sun Shirya ba Iran Makaman Nukiliya
- Rasha ta yi ikirarin cewa ƙasashen da dama sun nuna a shirye suke su bai wa Iran makaman nukiliya bayan harin da Amurka ta kai mata
- Mataimakin shugaban Majalisar Tsaron Rasha, Dmitry Medvedev ne ya bayyana hakan, ya ce Iran ta kara samun goyon baya daga ƙasashe
- Wannan kalamai na zuwa ne bayan Amurka ta tabbatar da kai hari wurare uku da Iran ke shirin nukiliya, lamarin da ya ja hankalin duniya
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Russia - Ƙasar Rasha ta bayyana cewa akwai ƙasashen da dama da suka nuna a shirye suke su bai wa Iran makaman nukiliya bayan hare-haren da Amurka ta kai.
Mataimakin shugaban majalisar tsaro na Rasha, Dmitry Medvedev, ya bayyana cewa wasu ƙasashe sun dawo tsagin Iran, sun fara shirin ba ta makaman nukiliya kai tsaye.

Asali: Getty Images
Harin Amurka a Iran ya fusata ƙasashe
TRT Afirka ta rahoto cewa Medvedev ya fitar da wannan bayani a wata sanarwa, yana mai cewa “Wasu ƙasashe na shirye-shiryen bai wa Iran makaman nukiliya kai tsaye.”
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan furuci ya zo ne bayan Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa sojojin Amurka sun kai hare-haren bama-bamai a wuraren nukiliya uku na ƙasar Iran.
Wuraren da Amurka ta jefa wa bama-baman sun haɗa da Fordow, Natanz, da Isfahan, cibiyoyi masu mahimmanci da Iran ke amfani da su wajen sarrafa nukiliya.
Iran na ci gaba da shirin habaka nukiliyarta
Medvedev ya ce duk da hare-haren ba su yi mummunan ɓarna sosai ba, akwai yuwuwar Iran ta ci gaba da sarrafa sinadarin uranium don samar da makaman nukiliya.
Ya ce hare-haren Amurka sun sa shugabannin Iran su ƙara karɓuwa a duniya, yana mai cewa wasu ƙasashe da ba su goyon bayansu a baya, yanzu sun dawo tsaginsu.
“Hatta waɗanda ba sa goyon bayan gwamnatin Iran yanzu sun dawo, sun mara mata baya,” in ji shi.
Rasha ta ƙara caccakar shugaban Amurka
Shugaban ya gargaɗi Amurka da cewa tana ƙoƙarin tsokano rikici mai girma wanda ba za ta iya jurewa ba, rahoton BBC News.
Medvedev ya soki Donald Trump kan sake jefa duniya cikin yaki, duk da cewa lokacin da ya tsaya neman takara a ƙaro na biyu, ya nuna shi mutum ne mai son zaman lafiya.

Asali: Getty Images
Ya ce wannan hali bai dace da mutumin da ke burin samun lambar yabo ta zaman lafiya ta Nobel ba.
Medvedev ya bayyana cewa ƙasashe da dama a duniya ba su goyon bayan hare-haren da Amurka da Isra’ila ke kai wa Iran.
Iran ta lalata wutar lantarki a Isra'ila
A wani labarin, kun ji cewa luguden wutar da ƙasar Iran ke ci gaba da yi wa yahudawa ya katse wutar lantarki a sassa daban-daban a Isra'ila.
An ruwaito cewa yahudawa sama da 8,000 na fama da matsanancin rashin wutar lantarki sakamakon harin ta Iran ƙai ƙasar Isra'ila.
Ministan makamashi na Isra'ila ya ce hukumomi sun riga sun shirya tun da farko don fuskantar irin wannan barazana, yana mai cewa za a maido da wutar a cikin awa uku.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng