Isra'ila Ta Amince da Tsagaita Wuta, Ta Gargadi Iran kan Kai Mata Hari
- Iran da Isra’ila sun amince da tsagaita wuta bayan kwanaki 12 ana musayar hare-haren sama masu zafi wanda ya jawo asarar rayuka da dama
- Shugaban Amurka, Donald Trump ne ya gabatar da shawarar tsagaita wutar, kuma Isra’ila ta amince da hakan tare da haɗin gwiwa da shi
- Iran ta harba makamai na karshe kafin lokacin tsagaita wuta ya kankama, inda ta ce an yi haka ne domin ladabtar da kasar Isra'ila
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Kasar Israel – Rahotanni sun bayyana cewa Iran da Isra’ila sun amince da tsagaita wuta bayan kwanaki 12 na musayar miyagun makamai da ya jawo asarar rayuka.
Ta cikin wata sanarwa da Firayim Minista Benjamin Netanyahu ya fitar da safiyar Talata, ya tabbatar da cewa Isra’ila ta amince da tsagaita.

Asali: Facebook
Aljazeera ta ruwaito cewa tun da farko, Shugaban Amurka, Donald Trump ya sanar da cewa kasashen biyu sun zo masa da bukatar a tsagaita wuta a tsakaninsu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Amurka ta sanar da tsagaita wuta
BBC ta ruwaito cewa sanarwar Isra’ila ta zo ne jim kaɗan bayan Trump ya wallafa a shafinsa na sada zumunta cewa an fara aiwatar da tsagaita wutar.
Shugaban Amurka ya wallafa cewa:
“Tsagaita wutar ta fara aiki yanzu. Ina roko kada a karya wannan yarjejeniya.”
Duk da haka, Netanyahu ya yi barazanar cewa Isra’ila za ta mayar da martani idan aka karya yarjejeniyar, amma amincewar da aka cimma na nuna alamun fatan samun sauƙin rikicin.
A cewarsa:
“Dangane da tabbatar da manufofinmu da cikakken haɗin gwiwa da Shugaba Trump, Isra’ila ta amince da shawarar Shugaban Amurka na tsagaita wuta tsakanin ɓangarorin biyu.”
An fara tsagaita wutar yakin Iran da Isra'ila
A safiyar yau Talata, rahotanni sun nuna cewa an ɗan samu natsuwa bayan hare-haren roka guda shida da Iran ta kaddamar, wanda hakan ke nuni da cewa rikicin na raguwa.

Asali: Getty Images
Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi, ya nuna cewa hare-haren sun faru ne kafin ƙarfe 07.30 na safe agogon GMT, wanda Trump ya ambata a matsayin lokacin iyakar kai harin.
Ya ce:
“Dakarunmu masu ƙarfi sun ci gaba da farmakin soji don ladabtar da Isra’ila saboda cin zarafinta har zuwa daƙiƙa ta ƙarshe."
Rahotanni daga hukumomin agaji da sojojin Isra’ila sun tabbatar da cewa wasu mutane sun rasa rayukansu a cikin harin.
Abin da ya sa Amurka tsoron Iran - Bukarti
A baya, mun wallafa cewa fitaccen lauya kuma mai fafutukar kare hakkin dan Adam, Bulama Bukarti, ya caccaki gwamnatin Amurka bisa kai hari kan ƙasar Iran ba tare da bin ka’ida ba.
A cewarsa, harin na Amurka wani yunkuri ne na gaggawa saboda tsoron tasirin da Iran ke da shi a fannin siyasa da tattalin arziki, yana mai cewa wannan ya saba dokokin kasa da kasa.
Dr. Bukarti ya bayyana cewa Amurka na jin tsoron yadda Iran ke da ƙarfi da iko da zirin Hormuz, wanda ya ce na daga cikin manyan hanyoyin jigilar danyen mai a duniya da ke shigar da mai kasashen Turai.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng