Kaikayi Koma kan Mashekiya: Yadda Kai Hari a Iran zai Shafi Tattalin Amurka
- Tattalin arzikin Amurka na fuskantar sabuwar barazana sakamakon tashin farashin mai bayan harin da ta kai kan wuraren nukiliya uku a Iran
- Masana sun ce farashin gangar danyen mai zai iya haura $80, wanda zai iya janyo hauhawar farashin man fetur da dizil a Amurka
- Baya ga haka, masana sun bayyana tsoron cewa idan Iran ta toshe mashigin ruwa na Hormuz, farashin gangar danyen mai zai iya haura $100
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
America - Tattalin arzikin Amurka na iya sake fuskantar hauhawar farashin kaya sakamakon harin jiragen sama kan cibiyoyin nukiliya na Iran.
Lamari na iya tayar da hankali a kasuwannin man fetur, musamman idan ya shafi hanyar ruwa ta Hormuz, wanda ke da muhimmanci a safarar kashi 20 cikin 100 na man da duniya ke bukata.

Asali: Getty Images
CNN ta wallafa cewa farashin danyen mai ya riga ya tashi da kashi 10 cikin 100 tun bayan harin da Isra’ila ta kai a ranar 13 ga Yuni.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hakan na zuwa ne bayan farashin ya ragu kadan bayan sanarwar Shugaba Donald Trump ta farko da ya ce zai duba yiwuwar kai hare-hare Iran cikin makonni biyu
Farashin mai zai shafi tattalin Amurka
Masanin a harkokin danyen mai, Andy Lipow ya bayyana cewa ana sa ran farashin gangar danyen mai zai kai $80.
A cewarsa, wannan shi ne karon farko da Amurka za ta fuskanci irin wannan hauhawa tun watan Janairu.
Mataimakin shugaban nazarin mai a dandalin GasBuddy, Patrick De Haan ya ce tashin farashin na iya shafar gidajen mai a Amurka cikin awanni idan hauhawan ya ci gaba.
A cewarsa:
“Idan farashin kasuwannin mai ya hau yau da gobe, farashi zai karu a gidajen mai cikin kwanaki biyar.”
Takaddama kan rufe hanyar Hormuz
Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi, ya bayyana cewa ƙasarsu tana da zaɓuɓɓuka da dama don mayar da martani kan harin da Amurka ta kai.
Tsohon mai ba Shugaban George W. Bush shawara kan makamashin duniya, Bob McNallyya ya ce idan Iran ta toshe Hormuz, hakan na iya janyo martani daga dakarun Amurka da kawayenta.
Rahoto ya nuna cewa Bob McNally ya ce hakan zai yi mummunan tasiri ga kasuwannin mai da iskar gas a yankin Gulf.
Ana hasashen hauhawar farashi a Amurka
Masana tattalin arziki na hasashen cewa hauhawar farashi zai ƙara muni cikin watanni uku masu zuwa, musamman saboda hauhawar farashin man fetur da manufofin Trump.
Babban mai nazari a kamfanin RSM, Joe Brusuelas ya ce:
“Hauhawar farashi na wannan lokacin na iya zama shiri ne ga wata guguwar hauhawar farashi da za ta biyo baya lokacin bazara.”
Amurka ta yi magana kan hanyar Hormuz
A wani rahoton, kun ji cewa kasar Amurka ta fara magana kan kokarin Iran na toshe hanyar ruwan Hormuz.
A kan haka ne ma Amurka ta ke bukatar kasar China ta shawo kan Iran wajen hana ta toshe hanyar ruwan.
Amurka ta ce toshe hanyar zai shafi tattalin kasashen yankin Asia da ke kusa da Iran da Isra'ila da ke fafatawa a fagen yaki.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng