'Akwai Barazana': Majalisar Dinkin Duniya Ta Yi Magana kan Harin Amurka a Iran

'Akwai Barazana': Majalisar Dinkin Duniya Ta Yi Magana kan Harin Amurka a Iran

  • Majalisar Dinkin Duniya ta soki hare-haren da Amurka ta kai kan Iran, tana cewa suna barazana ga zaman lafiya a duniya baki ɗaya
  • Sakataren MDD, Antonio Guterres ya ce yana cikin firgici saboda harin da jiragen yakin Amurka suka kai kan wuraren nukiliya a Iran
  • Ya bayyana cewa "wannan lokaci mai hadari ne", yana kira da a kauce wa rikicin da zai janyo bala’i ga fararen hula da duniya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Washington DC, Amurka - Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres ya yi magana kan harin Amurka a Iran.

Guterres ya yi Allah wadai da harin inda ya ce hakan kwata-kwata ba zai haifar da ɗa mai ido ba.

Majalisar Dinkin Duniya ta soki harin Amurka a Iran
Majalisar Dinkin Duniya ta yi Allah wadai da harin Amurka a Iran. Donald J Trump.
Asali: Getty Images

MDD ta yi Allah wadai da harin Amurka

Guterres ya bayyana wannan abin takaici ne a shafinsa na X a daren ranar Lahadi 22 ga watan Yunin 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sakataren ya ce yana “cikin firgici matuka” game da abin da ya kira mummunan harin Amurka kan Iran.

Ya bayyana cewa akwai hadarin da rikicin ke kara tabarbarewa cikin gaggawa da hakan zai iya haifar da babban bala’i ga fararen hula da duniya.

Ya ce a wannan lokaci mai matukar hadari, yana da muhimmanci a kauce wa rudani inda ya bukaci a ci gaba da kokarin diflomasiyya.

Sanarwar ta ce:

"Ina cikin matukar firgici game da amfani da karfi da Amurka ta yi a kan Iran a yau.
"Wannan mataki ne mai hadari a yankin da ke dab da rincabewa kuma barazana kai tsaye ga zaman lafiya da tsaro na duniya.
"Akwai hadarin da ke kara karfi cewa wannan rikici zai kubuce wa iko cikin sauri lamarin da zai iya janyo mummunan tasiri ga fararen hula, yankin, da duniya baki ɗaya.
Majalisar Dinkin Duniya ta soki harin Amurka a Iran
Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadi bayan Amurka ta kai hari Iran. Hoto: United Nations.
Asali: AFP

Kiran da Majalisar Dinkin Duniya ta yi

Antonio Guterres ya yi kira na musamman ga mambobin Majalisar Dinkin Duniya da su bi tsarin dokar majalisar wurin tabbatar da zaman lafiya.

Ya ce a daidai wannan lokaci ana bukatar hadin kai da kaucewa duk wata hanya da zai kara jawo rasa rayuka a ɓangarorin.

Ya kara da cewa:

"Ina kira ga kasashe mambobin Majalisar Dinkin Duniya da su sassauta wuta tare da kiyaye nauyin da ke kansu bisa dokar tsarin Majalisar Dinkin Duniya da sauran dokokin kasa da kasa.
"A wannan lokaci mai hadari, yana da matukar muhimmanci a kauce wa rikice-rikicen da za su janyo rudani mara iyaka.
"Babu mafita ta hanyar karfin soja, hanya daya da za a bi ita ce diflomasiyya, burin da ya rage shi ne zaman lafiya."

Iran/Isra'ila: MDD ta bukaci tsagaita wuta

Kun ji cewa Hukumar kare hakkin bil’adama ta Majalisar Dinkin Duniya ta nemi a gaggauta kawo karshen rikicin Iran da Isra’ila da tattaunawar diflomasiyya.

Hukumar ta ce ya zama dole a kare fararen hula yayin da hare-haren makamai ke cigaba da halaka mutane a birane.

Jakadan Iran ya ce hare-haren Isra’ila kan gine-ginen nukiliya barazana ne ga lafiyar jama'a, yana kira da a hukunta kasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.