Shekara 1 a Mulki: Majalisar Dinkin Duniya Ta Magantu Kan Mulkin Tinubu, Ta Jero Nasarori

Shekara 1 a Mulki: Majalisar Dinkin Duniya Ta Magantu Kan Mulkin Tinubu, Ta Jero Nasarori

  • Yayin da Shugaba Bola Tinubu Tinubu ke neman shekara daya a mulki, Majalisar Dinkin Duniya ta yi martani kan salon mulkinsa
  • Majalisar ta ce gwamnatin Bola Tinubu ta yi namijin kokari wurin tabbatar da inganta tattalin arziki da kuma dakile matsalar tsaro
  • Wannan na daga cikin jawabin mataimakiyar Sakataren Majalisar, Hajiya Amina Mohammed inda ta yabawa gwamnatin kan tsare-tsarenta

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Majalisar Dinkin Duniya ta yi martani kan ci gaban da aka samu a gwamnatin Bola Tinubu.

Majalisar ta ce an samu ci gaba matuka ta bangaren tattalin arziki da kuma matsalar tsaro da ya addabi kasar.

Kara karanta wannan

"Yana hawa Najeriya ta durkushe": Tsohon Sakataren Gwamnatin Buhari ya soki Tinubu

Majalisar Dinkin Duniya ta yabawa gwamnatin Tinubu
Majalisar Dinkin Duniya ta ce Bola Tinubu ya inganta tsaro da tattalin arziki. Hoto: @officialABAT.
Asali: Twitter

UN: Nasarori da Tinubu ya kawo Najeriya

Mataimakiyar Sakataren Majalisar, Hajiya Amina Mohammed ita ta bayyana haka inda ta ce a cikin shekara daya na mulkin Tinubu an samu gagarumar nasara.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Amina ta ce Tinubu ya yi kokarin daidaita tattalin arzikin kasar duba da yadda ya ke daukar wasu matakai da suke taimakawa, cewar rahoton Vanguard.

Tsohuwar Ministar ta ce a bangaren tsaron kasar kuwa gwamnatin Tinubu ta dauki matakai domin dakile matsalar a kasar baki daya, Pulse ta tattaro.

Tinubu yana kokarin inganta rayuwar 'yan Najeriya

Hajiya Amina ta bayyana haka ne yayin wani babban taro a Abuja da ya shafi inganta rayuwar yan Najeriya.

Ta yabawa Tinubu a cikin shekara daya da ya yi kan karagar mulki wurin tabbatar da daidaita lamuran kasar baki daya.

Wannan martani na zuwa ne yayin da ƴan Najeriya ke kokawa kan mawuyacin hali da suke ciki a kasar musamman tsadar kayayyakin abinci.

Kara karanta wannan

Yayin da ake kukan tsadar kujerar hajji, Tinubu ya tausaya da tallafin biliyoyi

Al-Mustapha ya magantu kan matsalar tsaro

A wani labari, kun ji cewa tsohon dogarin marigayi Sani Abacha, Manjo Hamza Al-Mustapha ya yi martani kan matsalar tsaron Najeriya da ya yi katuru.

Al-Mustapha ya ce babban matsalar da aka samu shi ne rashin yin wani katabus daga gwamnatocin baya sauka gabata a Najeriya.

Ya ce an tafka kuskure wurin barin matsalar ta girma kamar haka wanda ke buƙatar yin amfani da dabarun kimiyya wurin dakile matsalar a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.