Iran Ta Sake Fuskantar Matsala a Yaƙinta da Isra'ila, An Farmaki Babban Asibiti a Tehran

Iran Ta Sake Fuskantar Matsala a Yaƙinta da Isra'ila, An Farmaki Babban Asibiti a Tehran

  • Hukumomin kasar Iran sun tabbatar da cewa Isra'ila ta kai farmaki kan asibiti na uku a Tehran, babban birnin Jamhuriyar Musulunci
  • Ma'aikatar lafiya ta Iran ta bayyana cewa harin ya lalata motocin ujila, waɗanda ake amfani da su wajen ɗaukar marasa lafiya
  • Ta buƙaci kungiyoyin lafiya na duniya kamar WHO da su tashi tsaye, su yi koƙarin kare lafiyar asibitoci, likitoci da marasa lafiya

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Iran - Ma’aikatar Lafiya ta Ƙasar Iran ta sanar da cewa wani asibiti da ke Tehran, babban birnin ƙasar, ya fuskanci sabon hari daga Isra’ila.

Wannan hari da Isra'ila ta kai kan asibiti a Tehran ya ƙara rura wutar rikicin da ke ci gaba da ɗaukar hankalin duniya tsakanin ƙasashen biyu.

Jagoran addinin Iran, Ali Khamenei.
Isra'ila ta kai hari kan Asibiti na uku a Tehran Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

A cewar shugaban sashen hulɗa da jama’a na Ma’aikatar Lafiya, wannan shi ne asibiti na uku da ya gamu da irin wannan hari a ƙasar cikin kwanaki bakwai da suka gabata, rahoton Alzajeera.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Isra'ila ta kai hari asibiti na 3 a Tehran

"Wannan shi ne karo na uku da asibiti ke fuskantar hari a Iran. Haka kuma, motocin ujila uku na daukar marasa lafiya a wata cibiyar kiwon lafiya ta musamman suma sun sha luguden wuta daga abokan gaba,” in ji hukumomin Iran.

Ma’aikatar ta zargi Isra’ila da laifin take dokokin kasa da kasa, tana mai cewa:

"A cikin kwanaki bakwai da fara wannan ɗabi'a ta rashin imani, Isra’ila ta karya dokokin kasa da kasa fiye da sau shida.”

Ɓarnar da harin Isra'ila ta yi a asibiti

Sanarwar ta bayyana cewa harin da aka kai bai tsaya iya asibiti kawai ba, har da muhimman kayan aiki da ke taimaka wa marasa lafiya da jama’ar gari gaba ɗaya.

Wannan na zuwa a daidai lokacin da rikici ke kara tsananta a Gabas ta Tsakiya, lamarin da ke jefa lafiyar jama’a da tsaron fararen hula cikin barazana mai tsanani.

A cewar hukumomin Iran, asibitocin da aka kai wa hari a baya sun hada da asibitin da ke kusa da kan iyakar Yamma da Iraq, asibitin lardin Khuzestan da kuma na Tehran.

Shugabannin Iran da Isra'ila.
Iran ta buƙaci kungiyoyin lafiya na duniya su taka wa Isra'ila birki Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Iran ta aika sako da WHO da ƙungiyoyi

Ma’aikatar Lafiya ta Iran ta yi kira ga kungiyoyin lafiya na duniya da su yi gaggawar kawo ɗauki domin kare asibitoci daga sharrin Isra'ila, BBC News ta rahoto.

Ta yi kira ga Kungiyar Lafiya ta Duniya (WHO) da Kungiyar Agaji ta Ƙasa da Ƙasa (ICRC), da su kare asibitoci, ma’aikatan lafiya da kuma marasa lafiya daga hare-haren da ke kara tsananta.

"Wannan ba kawai hari ne akan gine-gine ba, hari ne mai haɗari ga rayuwar marasa lafiya da ma’aikatan lafiya,” in ji sanarwar.

Yahudawa sama da 8,000 sun rasa gidajensu

A wani rahoton, kun ji cewa sama da Isra’ilawa 8,000 sun rasa matsuguninsu sakamakon hare-haren ramuwar gayya da Iran ke ci gaba da kai wa a ƙasar.

Alƙaluman asusun diyya da harajin dukiyoyi na Isra'ila ya nuna cewa mutane sama da 30,000 suka shigar da buƙatun neman diyyar gine-ginesu da aka rusa.

Wannan adadi mai yawa na yahudawan Isra'ila da suka rasa matsuguninsu yana nuna irin mummunar illar da rikicin ke haifarwa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262