Hukuncin da Kotu Ta Yanke wa Mutumin da Aka Kama a Bidiyo Yana Kona Alkur'ani
- Wani dan asalin Turkiyya mai suna Hamit Coskun ya kona Alƙur’ani a Landan yana mai cewa addinin Islama addinin ta'addanci ne
- Kotu ta tabbatar da cewa Coskun ya aikata laifi bisa ƙiyayya ga Musulmi, abin da ya saba wa dokokin Birtaniya na zaman lafiya
- Wannan hukuncin ya janyo cece-kuce, inda kungiyoyin da suka tsaya masa suke ganin hakan hari ne ga 'yancin faɗar albarkacin baki
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Birtaniya - Kotu ta samu wani dan asalin Turkiyya da ya kona Alƙur’ani a birnin Landan, da laifin tayar da fitina bisa dalilin ƙiyayya ga wani addini a ranar Litinin.
A cikin wani bidiyo, an nuna Hamit Coskun yana cewa: "Addinin Islama addinin ta'addanci ne" da kuma "Ga shi ina kona Alƙur’ani", yayin da ya cinnawa Alƙur’anin wuta a gaban ofishin jakadancin Turkiyya da ke Landan, ranar 13 ga Fabrairu.

Asali: Twitter
Kotu ta samu Baturke da laifi bayan kona Alkur'ani
Coskun mai shekara 50 ya ce yana suka ne kawai ga addinin Islama ba ga mabiyansa ba, amma alkalin kotun Westminster Magistrates, John McGarva, ya ce bai gamsu da hakan ba, inji rahoton Times of India.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Alkalin ya samu Coskun da laifin aikata dabi’ar rashin kunya a bainar jama’a “a inda mutum zai iya jin ko ganin abin da zai firgita ko tada hankalinsa.”
McGarva ya ce Coskun ya aikata wannan ne “saboda ƙiyayya ga mabiya wani addini, watau Musulmi,” wanda ya saba da dokar Crime and Disorder Act ta 1998 da kuma sashi na biyar na dokar Public Order Act ta 1986.
Hukuncin da kotu ta yanke wa Coskun
Mai shari'a McGarva, wanda ya ci tarar Coskun fam 240 (£240) da kuma ƙarin haraji na doka fam 96 (£96), ya kara da cewa:
“Ayyukanka na kona Alƙur’ani a wurin da ka aikata hakan suna da matuƙar tayar da hankali, kuma ka ƙara da faɗin kalmomin batanci da ƙiyayya ga addinin, alamar cewa kana da ƙiyayya da mabiyansa.”
Masu shigar da ƙara daga gwamnati sun jaddada cewa ba a gurfanar da Coskun bane saboda kona Alƙur’ani.
“An gurfanar da shi ne saboda rashin kunya da nuna ɗabi’a marar kyau a bainar jama’a,” in ji Philip McGhee, mai gabatar da ƙara daga bangaren gwamnati.
An ga bidiyon Coskun yana kona Alkur'ani
Coskun ya baro Midlands, ya tafi har Rutland Gardens, Knightsbridge, a ranar 13 ga Fabrairu, inda ya aikata wannan laifi.
Duk da nadarsa a bidiyo, ya shaida wa kotun cewa ya yi hakan ne cikin lumana, kuma kona Alƙur’ani da ya yi wani nau’in faɗar albarkacin baki ne.
Wani mutumi da yake wucewa kusa da wurin ne ya ɗauki bidiyon lamarin, inda aka gani wani mutum da ake zargin yana rike da wuka ya tunkari Coskun ya kuma yi ƙoƙarin kai masa hari.
Coskun, wanda yanzu haka yake neman mafaka a Birtaniya, ya wallafa a kafafen sada zumunta cewa yana zanga-zanga ne kan “gwamnatin ‘yan Islama” ta Shugaba Recep Tayyip Erdogan na Turkiyya.

Asali: Twitter
An caccaki alkali kan hukunta Coskun
Kungiyar kare fadar albarkacin baki (FSU) da kungiyar NSS ne suke ɗaukar nauyin lauyoyin Coskun, kuma sun ce yana fuskantar shari’a ne ta batanci ga addini, duk da cewa Birtaniya tana da dokar kare 'yancin faɗar albarkacin baki.
FSU ta bayyana hukuncin kotun a shafinta na X da cewa:
"Wannan hukunci hari ne kan ’yancin faɗar albarkacin baki, kuma zai hana wasu su yi amfani da haƙƙinsu na zanga-zangar lumana da bayyana ra’ayinsu."
“Kowa na da ’yancin zanga-zanga cikin lumana da bayyana ra’ayinsa, komai tsanani ko ɓacin ran da hakan zai jawo wa wasu.”
Alkur'ani a idon Musulmai
Alƙur’ani mai girma shi ne tushen rayuwa da jagora ga dukkan Musulmai a duniya. Wannan littafi ne mai tsarki da Allah (SWT) ya saukar wa Annabi Muhammad (SAW) ta hanyar Mala’ika Jibril, domin shiryar da al’umma zuwa ga gaskiya da ceto a duniya da lahira.
Musulmai suna daraja Alƙur’ani fiye da komai; suna ɗaukar sa da tsarki, suna karanta shi da ladabi, kuma ana horar da yara tun ƙuruciya su haddace shi.
Saboda girman da Alƙur’ani ke da shi a zuciyar Musulmi, duk wani abu da ya shafi raini ko cin zarafin wannan littafi na iya tayar da hankali da fusata Musulmai a ko’ina cikin duniya.
Yadda wasu ke wulakanta Alkur'ani
A 'yan shekarun nan, an sha samun wasu da ke kona ko tozarta Alƙur’ani a kasashen Turai da wasu sassan duniya da nufin tayar da husuma ko nuna ƙiyayya ga Musulmi.
Wannan hali na nuna wulakanta Alƙur’ani galibi ana kallonsa a matsayin ƙiyayya da tsokana wadda ke iya tayar da rikici da nuna wariya.
Musulmai da dama suna ganin irin waɗannan ayyuka a matsayin harin kai tsaye ga addininsu da kuma tunaninsu na tsarki.
An kashe baturen da ya kona Alkur'ani
A wani labarin, mun ruwaito cewa an kashe Salwan Momika a Sweden, mutumin da ya haddasa rikici bayan kona Alƙur'ani a 2023.
Firaministan Sweden ya bayyana yiwuwar cewa kisan yana da nasaba da kasashen waje, inda ya ce hukumomi na ci gaba da bincike.
Wasu kafafen labarai a Södertälje, kusa da Stockholm, sun bayyana cewa 'yan bindiga ne suka shiga gidan Salwan suka harbe shi har lahira.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng