Sabon tashin hankali ya kunno kai a Sweden yayin da wasu ke shirin kone Al-Qur'ani

Sabon tashin hankali ya kunno kai a Sweden yayin da wasu ke shirin kone Al-Qur'ani

  • An samu tashin-tashina a kasar Sweden tun bayan da wata kungiya ta tsiri shirin kona Al-Qur'ani mai girma
  • Al-Qurani dai littafi ne da aka saukarwa Annabin karshen zamani (SAW), wanda masu nuna kiyayya ga muslunci ke gangamin konawa
  • Lamarin da jawo hargitsi, inda aka samu zubar jini da kuma raunuka da dama a wasu sassan kasar ta Sweden

Stockholm, Sweden- Aniyar wata kungiya mai kiyayya ga Musulunci na kona kwafin mushafin Al-Qur'ani a bainar jama'a ya haifar da mummunan artabu da masu zanga-zanga a kwana na uku a kasar Sweden, in ji 'yan sanda a ranar Lahadi.

Sanarwar da ‘yan sandan ta fitar ta ce, an kona rumfunan shara, da motar bas da kuma wata mota a wasu jerin tashin tashina da suka faru a kudancin birnin Malmo cikin dare, inji Arab News.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Jami'in tsaro daya ya mutu yayin da sojoji suka ragargaji 'yan bindiga a Neja

Kakakin 'yan sanda Kim Hild ta shaida wa gidan rediyon jama'a na SR cewa lamarin ya dan lafa, ta kara da cewa babu wani jami'in da ya samu rauni, amma da dama daga cikin jama'a sun samu raunuka.

Rikici kan batun kone Qur'ani
Sabon tashin hankali ya kunno kai a Sweden yayin da wasu ke shirin kone Al-Qur'ani | Hoto: www.france24.com
Asali: UGC

Kusan korafe-korafe 20 ne aka shigar gaban hukuma ciki har da barna.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A 'yan kwanakin nan dai an sha samun irin wannan rikici dangane da shirin da kungiyar Stram Kurs (Hard Line) mai kyamar baki da addinin Islama karkashin jagorancin dan siyasar Denmark Rasmus Paludan ke jagoranta na kona kwafin al-Qur'ani a bainar jama'a.

Rikicin da ya kunno a ranar Asabar ya barke ne bayan wani gangami da magoya bayan kungiyar suka gudanar a ranar.

An kai jami’an ‘yan sanda uku asibiti bayan wani tarzoma da ya barke a birnin Linkoping da ke gabashin Sweden ranar Alhamis. An kama mutane biyu a wannan zanga-zangar.

Kara karanta wannan

Harin 'yan bindiga a Plateau: Ya zuwa yanzu mun binne mutane 106, inji shugaban karamar hukuma

Kana a ranar Juma'a, 'yan sanda 9 sun jikkata a irin wannan tashin-tashina da aka yi a Orebro da ke tsakiyar kasar Sweden.

Kasar Iraki ta sa baki

A ci gaba da tabarbarewar al'amura, ma'aikatar harkokin wajen Iraki ta ce ta gayyaci jami'an kula da harkokin Sweden a Bagadaza ranar Lahadi don tattaunawa.

Ya yi gargadin cewa lamarin na iya haifar da "mummunan sakamako" kan "dangantakar da ke tsakanin Sweden da Musulmai gaba daya, kasashen musulmi da na Larabawa da kuma al'ummar musulmi a Turai."

Paludan na shirin sake gudanar da taruka a wasu garuruwa biyu na kasar Sweden, amma irin wannan aika-aikata ba ta samu izini daga 'yan sanda ba.

Shi dai Paludan a shekarar 2019, ya kona Al-Qur'ani bayan lullube shi da naman alade, lamarin da ya kai Facebook ya rufe shafinsa na tsawon wata guda bayan wani sakon da aka rubuta da ke bayyana mummunan aiki, kamar yadda France24 ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Amurka ta amince Buhari ya kashe $1bn domin shigo da wasu jiragen yaki

Fitaccen Malami a Saudiyya ya ce babu laifi yin bikin ranar zagayowar haihuwa a Musulunci

A wani labarin, Dr. Qais Bin Muhammad Al-Sheikh Mubarak, tsohon mamban kungiyar manyan malaman Saudi Arabiya, ya ce babu laifi idan musulmi ya yi murnar shagalin bikin al'ada irin su, murnar zagayowar haihuwarsa ko na masoyansa.

Jaridar Saudi Gazette ta ruwaito cewa, hakan bai da bambamci da murnar zagayowar ranar aure, samun karin girma ko matsayin mutum ko na 'ya'ya, samun damar kammala digiri ko kammala karatu daga jami'a, ko sauran bukukuwa, a cewarsa.

Kamar yadda Al-Mubarak ya bayyana, babban abu game da bukukuwan nan shine, abubu aya ko hadisi da ya halasta ko ya haramta hakan. Ya dauki wadannan tarukan a matsayin wani bangare na al'ada, wadanda basu da wani aibu a addinance.

Asali: Legit.ng

Online view pixel