"Ban San Laifi Bane" Abdulazeez Wanda Ya Ƙona Alƙur'ani a Arewa Ya Aike Da Sako Ga Musulmai

"Ban San Laifi Bane" Abdulazeez Wanda Ya Ƙona Alƙur'ani a Arewa Ya Aike Da Sako Ga Musulmai

  • Abdulazeez Adegbola, ɗan addinin gargajiya da ake zargi da ƙona Alƙur'ani a jihar Kwara ya roƙi Musulman Najeriya su yafe masa
  • Ya bayyana cewa bai san ƙona Alƙur'ani laifi ne mai girma ba amma ya ɗauki Alkawarin ba zai sake aikata hakan ba
  • Mutumin na fuskantar shari'a hudu kan kona littafin Allah mai tsarki watau Alƙur'ani da kuma ɓata suna a jihar Kwara

Ahmad Yusuf, kwararren Edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kwara - Fitaccen ɗan addinin gargajiya, Abdulazeez Adegbola, wanda aka fi sani da Tani Olohun, ya roƙi waɗanda suka gurfanar da shi a gaban Kotu da kafatanin Musulman Najeriya su yafe masa.

Abdulazeez Adegbola.
‘Ban San Kona Kur’ani Laifi Ne Ba,’ Abdulaziz Ya Roki Musulmi Su Yafe Masa Hoto: Dailytrust
Asali: UGC

Abdulazeez ya roki Al'ummar Musulmai su yafe masa bisa laifin ƙona Alƙur'ani mai tsarki da kuma cin mutunci da ɓata sunan wasu Musulmai a jihar Kwara.

Kara karanta wannan

Zaben Kano: Tinubu ya shiga babbar matsala kan tsige Gwamna Abba Gida-Gida

Ɗan addinin gargajiyan ya nemi afuwa ne yayin da yake jawabi a Kotu jim kaɗan bayan an bada belinsa ranar Alhamis, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A kalamansa ya ce:

"Ban san ƙona Alƙur'ani babban laifi bane, amma ana sanar dani ban yi wata- wata ba na goge bidiyon abin da na aikata daga shafina na soshiyal midiya cikin ƙasa da minti ɗaya."
"Ina roƙon dukkan waɗanda suka shigar da ƙarata da al'ummar Musulmi baki ɗaya su yafe mun, na yi alƙawarin ba zan sake maimaita irin haka na wallafa a dandalin sada zumunta ba."

Yadda Kotun ta bada belinsa

Tun da farko, Kotun ƙarƙashin jagorancin mai shari'a A.S Adam, inda Tani Olohun ke fuskantar shari'a biyu, ta bada belinsa kan kudi Naira miliyan biyu da kuma mutum uku da zasu tsaya masa.

Kara karanta wannan

Yajin NLC: Harkoki sun tsaya cak yayin da ma'aikata suka zaɓa wa kansu mafita a babban birnin jihar PDP

A sharaɗin belin da Kotu ta gindaya masa, ya zama dole ya kasance biyu daga cikin mutanen da zasu tsaya masa sun mallaki kadara a kewayen wurin da Kotun ke zama ko a jihar Oyo.

Daga nan kuma Alkalin ya ɗage sauraron ƙararrakin zuwa ranar 9 ga watan Janairu, 2023, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Matakin da Musulmai suka ɗauka a kansa tun farko?

Bisa wannan ci gaban, Tani Olohun ya samu beli daga shari’o’i daban-daban guda hudu a kotuna uku da ake tuhumar sa da laifin bata suna da kuma kona Alkur’ani a Ilorin.

Ƙararraki biyu da aka saurara ranar Alhamis sun haɗa karar Sheikh Labeeb Lagbaji da ta makarantar Modrasat Muhammed karkashin Farfesa Abubakar Aliagan suka shigar da shi.

Sun shigar da waɗannan ƙararaki ne bisa tuhumar mutumin da laifin ƙona Alƙur'ani mai girma da wasu ƙarin tuhume-tuhume.

Legit Hausa ta tattauna da wasu Musulmai kan wannan lamari, inda wasu suka nuna wannan laifi ne tsakaninsa da Allah, wasu kuma na gani a ɗauki mataki a kansa.

Kara karanta wannan

"Lokacin Mu Ne a Kogi": Yadda ƙabilu 3 ke neman ɗarewa mulkin jihar Kogi

Malam Lawan ya faɗa wa wakilin mu cewa shi a ganinsa ya kamata a hukunta shi domin hakan ya zama izina ga ƴan baya, amma duk da haka ya masa addu'ar shiriya.

A nasa hangen, Muhammad Abdullahi, ya ce Aƙur'ani littafin Allah ne, don haka a kyale shi da Allah domin dama ya yi alƙawarin kare Littafinsa.

"A bar shi da Allah kawai, tun a duniya zai gani domin Allah SWT ya yi alƙawarin kare Littafinsa, amma a zahirin gaskiya abun dole ya tunzur Musulmai," in ji shi.

Gwamnan PDP ya yi watsi da umarnin Kotu

A wani rahoton kuma Gwamna Adeleke ya kauce wa umarnin Kotun ɗa'ar ma'aikata wadda ta hana shi korar shugabar alƙalan jihar Osun, Oyebola Oyo.

A wata sanarwa da mai magana da yawunsa ya fitar, Gwamna Adeleke ya dakatar da ita kuma ya naɗa wanda zai maye gurbinta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel