Hajji ibadar Allah: Gwamnatin kasar Birtaniya ta tura Sojojinta don gabatar da aikin Hajji

Hajji ibadar Allah: Gwamnatin kasar Birtaniya ta tura Sojojinta don gabatar da aikin Hajji

Rundunar Sojan Birtaniya ta aika da dakarunta Musulmai zuwa kasar Makkah don su gabatar da aikin Hajji, tare da daukan nauyinsu don cika wannan muhimmin shikashikan addinin Musulunci, inji rahoton BBC Hausa.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito wannan ne karo na hudu da rundunar take aikawa da Sojojinta zuwa Saudiyya don aikin Hajji, inda a shirin da aka yi, rundunar Sojin kasar Saudi ne zata zamo mai masaukin bakin nasu.

KU KARANTA: Inyamurai sun dingaya ma Buhari sharudddan samun goyon bayansu a zaben shekarar 2019

Hajji ibadar Allah: Gwamnatin kasar Birtaniya ta tura Sojojinta don gabatar da aikin Hajji
Sojojin

Sai dai wannan wani lamari ne bambarakwai da ba’a saba ganin hakan ba musamman game da Sojoji, sakamakon idan har wani Soja ya tafi wata kasa, lallai ba zai wuce don samun horo ba, ko kuwa don yaki, amma sai ga shi a wannan karon aikin Hajji za su je.

Wani kwamandan Soja kuma Likita, Mansur Khan ya bayyana jin dadinsa da wannan mataki, inda yace: “Hajji wani ibada ne da miliyoyin Musulmai ke haduwa ba tare da wani tunanin abin Duniya ba, face don Ibadan Allah.”

Wannan mataki an dauke shi ne don janyo Musulmai zuwa shiga aikin Soja, da ma sauran addinai daban daban, tare da basu tabbacin za’a kare musu hakkokinsu da bukatun addinansu, sai dai duk da haka, wasu Musulman Birtaniya na ganin musulunci ba zai hadu da aikin Soja ba.

Amma a cewar wani Limamin Sojoji Musulmai, wanda shima Soja ne, Ali Omar ya musanta wannan tunani, inda yace: “Rundunar Sojan Birtaniya ta dauki Limamai don tabbatar da an kula da bukatun Sojoji Musulmai, kuma ina daya daga cikinsu.”

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng