Jerin Sanannun 'Kasashe 9 masu Makaman Nukiliya a Duniya

Jerin Sanannun 'Kasashe 9 masu Makaman Nukiliya a Duniya

A yau cikin kalace-kalacen rahotanni da sahfin jaridar Legit.ng ta saba gudanarwa ta kawo mu ku jerin wasu sanannun kasashen Duniya 9 ma su tarin Makaman Nukiliya na kare dangi.

Kamar yadda shafin jaridar Newsweek ya bayyana a ranar Talatar da ta gabata, jerin sanannun Kasashe 9 na Duniya masu Makaman Nukiliya sun hadar da; Rasha, Amurka, Faransa, Sin, Birtaniya, Pakistan, India, Isra'ila da kuma Koriya ta Arewa.

Jerin Sanannun 'Kasashe 9 masu Makaman Nukiliya a Duniya
Jerin Sanannun 'Kasashe 9 masu Makaman Nukiliya a Duniya

Jaridar ta kuma fayyace karara adadin Makaman Nukiliya da kowace Kasa cikin Kasashen 9 ta mallaka kamar haka;

1. Rasha - 6, 800

2. Amurka - 6, 600

3. Faransa - 300

4. Sin - 270

5. Birtaniya - 215

6. Pakistan - 140

7. India - 130

8. Isra'ila - 80

9. Koriya ta Arewa - 20

KARANTA KUMA: Wani Hatsari ya salwantar da Rayuwar Mutane 8 bayan dawowar su daga 'Kasar Andalus

Rahotanni sun bayyana cewa cikin kwana-kwanan nan akwai yiwuwar adadin wannan kasashe ya koma takwas sakamakon shugaban kasar Koriya ta Arewa, Kim Jong Un, da ya kulla yarjejeniya da shugaban Kasa Amurka, Donald Trump, na tarwatsa Makaman Kasar sa.

A sakamakon wannan yarjejeniya shugaban Kasar Amurka a nasa bangaren zai dakatar yaƙe-yaƙe da Kasar Koriya ta Kudu.

A yayin haka kuma jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje, ya bi sahun takwaran sa na jihar Kebbi, Abubakar Atiku Bagudu, wajen biyan albashin watan Yuni ga ma'aikatan jihohin su domin samun dama da gudanar da bikin Sallah cikin annashuwa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel