Wole Soyinka ya fadi abinda zai iya haddasa yakin duniya na 3

Wole Soyinka ya fadi abinda zai iya haddasa yakin duniya na 3

- Farfesa Wole Soyinka ya bayani a kan illoli da matsalar yada labaran karya

- Soyinka ya yi jawabi mai tsawo a kan matsalar labaran karya a wani shirin kafar watsa labarai ta BBC

- Farfesan ya ce irin labaran karya da ake yadawa a Najeriya zasu iya haddasa yakin duniya III

Farfesa Wole Soyinka, ya ce kirkira da yada labarai na karya ya zama babbar matsala, ga dan adam, da zata iya haddasa yakin duniya III.

Soyinka ya bayyana hakan ne a Abuja yayin da ya kasance bako na musamman a wani shirin kafar yada labarai ta BBC a kan illoli da matsalolin yada labaran karya.

A cewar sa, "na taba fadin cewar labarin bogi zai iya haddasa yakin duniya na III kuma dan Najeriya ne zai kirkire shi."

Farfesan ya ce shi kansa ya sha karanta labaran karya da aka alakanta su da shi.

Wole Soyinka ya fadi abinda zai iya haddasa yakin duniya na 3
Wole Soyinka
Asali: Depositphotos

Ya kara da cewa, "lokacin yakin neman zabe a shekarar 2015 an taba wallafa rahoton cewar na yiwa tsohon shugaban kasa Jonathan gori a kan auren mace marar ilimi.

"A wasu lokutan ma an wallafa cewar na kira iyayen wasu jama'a dabbobi saboda sun zabi wani dan takara."

DUBA WANNAN: Dalilin da yasa 'yan bindiga suka addabi jihohin Katsina da Zamfara - Masari

Soyinka ya ce ko a cikin shekarar da ta gabata ya ga labarai a dandalin sada zumunta dake yada cewar ya mutu.

Batun kirkira da yada labaran bogi na cigaba da bawa gwamnati da jama'a damuwa a Najeriya.

Ko a kwanakin baya sai da 'yan majalisar tarayya suka nemi a yi doka a kan kirkira da yada labaran bogi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng