Namibia ta fi kowace kasa a nahiyar Afirka tituna masu kyau - Africa Facts Zone

Namibia ta fi kowace kasa a nahiyar Afirka tituna masu kyau - Africa Facts Zone

- Najeriya ba ta samu shiga ba cikin jerin manyan kasashe 13 na Afirka da ke da kyawawan tituna a Afirka yayin da Namibia ta ciri tuta

- Seychelles, Eswatini, da Cape Verde sun kasance a mataki na 11, 12 da 13 a jere da juna.

- Kasar Afirka ta Kudu tana mataki na shida, yayin da Senegal da Kenya suke kan mataki na bakwai da na takwas a jerin

Shafin Africa Facts Zone mai fidda kididdiga kan sha'ani da al'amuran da suka shafi kasashen nahiyyar Afirka, ya bayyana jerin kasashen nahiyar mafiya kyawun tituna.

Kamar yadda Hukumar tattalin arziki ta duniya WEF ta fitar a kididdigar ta 2019, ta bayyana wasu kasashen Afrika 13 masu nagartattun tituna gwanin sha'awa.

Africa Facts Zone ta wallafa jerin kasashe 13 mafi kyawaun tituna a nahiyyar Afrika.

Kasar Namibia ta ciri tura, yayin da ta yiwa dukkanin kasashen Afrika zarra da fintikau ta mafi kyawun tituna luwai-luwai gwanin sha'awa.

Kasar Masar mai kayatuttun gine-gine ta biyo baya a mataki na biyu cikin jerin kasashin nahiyar Afrika da suka fi kowanne tituna masu kyau.

Namibia ta fi kowace kasa a nahiyar Afirka tituna masu kyau - Africa Facts Zone
Namibia ta fi kowace kasa a nahiyar Afirka tituna masu kyau - Africa Facts Zone
Asali: UGC

KARANTA KUMA: Sojoji sun ci gaba da yi wa mayakan Boko Haram kisan kare dangi a Arewa maso Gabas

Sauran kasashen da suka fito a sahu biyar na farko sun hadar da Rwanda, Morocco, da Mauritius.

Kasashe irin su Kenya, Senegal, Afrika ta Kudu, Algeria da kuma Tanzania, su ma ba a barsu a baya ba, cikin jerin kasashen da gwamnatocinsu suka inganta musu tituna.

Ga jerin kasashen 13 da matakin kowace kasa kamar haka:

1. Namibia

2. Egypt

3. Rwanda

4. Morocco

5. Mauritius

6. South Africa

7. Senegal

8. Kenya

9. Tanzania

10. Algeria

11. Seychelles

12. Eswatini

13. Cape Verde

DUBA WANNAN: Yadda za ka rika samun labaran Legit.ng Hausa a shafinka ana wallafawa

A baya Legit.ng ta kawo muku jerin kasashe 10 na nahiyyar Afrika da wutar lantarka ta wadata.

Cikin jerin kasashen, Mauritius da Tunisia su na samun wuta dari bisa dari inda hasken lantarki ko gizau ba ya yi.

Haka nan kuma ba a bar kasar Masar, Algeria, Morocco da Seychelles a baya ba, inda sai an kai ruwa rana kafin hasken lantarki ya yi raurawa a cikinsu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel