'Za Mu Iya': Tinubu Ya Dauki Mataki da Amurka Ta Janye Tallafin Yaki da Cutar HIV

'Za Mu Iya': Tinubu Ya Dauki Mataki da Amurka Ta Janye Tallafin Yaki da Cutar HIV

  • Majalisar zartarwa ta amince da ware N4.5bn don sayen magungunan HIV domin tallafa wa ‘yan Najeriya masu cutar kanjamau
  • Ministan lafiya, Ali Pate, ya ce wannan shiri zai tabbatar da cewa masu cutar HIV suna samun magani ba tare da wani katsewa ba
  • FEC ta kafa kwamitin wakilai daga ma’aikatun gwamnati daban-daban don samar da tsari mai dorewa kan kula da lafiyar jama’a

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Majalisar zartarwa ta tarayya (FEC) ta amince da ware N4.5bn don sayen magungunan HIV domin tallafa wa 'yan Najeriya masu cutar kanjamau.

Wannan matakin ya biyo bayan izinin gaggawa daga gwamnatin Amurka, wanda ya soke dakatar da tallafin kula da masu HIV a kasashe masu tasowa.

Tinubu ya jagoranci taron majalisar zartarwa, an ware kudin sayen magungunan HIV
Majalisar zartarwa ta tarayya ta amince a kashe N4.5bn don sayen magungunan HIV. Hoto: @NGRPresident
Asali: Twitter

Najeriya ta ware kudi don yaki da cutar HIV

Kara karanta wannan

Bayan shawarar gwamnoni, majalisa za ta zauna domin tabbatar da kudirin haraji da gaggawa

Dakatarwar ta fito ne daga umarnin Shugaba Donald Trump, a matsayin wani bangare na sake duba tallafin da Amurka ke bayarwa ga kasashen waje, inji rahoton The Cable.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Najeriya ta dogara sosai kan tallafin kasa da kasa wajen yaki da cutar HIV, musamman daga shirin PEPFAR na gwamnatin Amurka na tallafa wa masu kanjamau.

Gwamnatin tarayya ta ce kudin da aka ware zai ba da damar sayo fakitin magani 150,000 na HIV a cikin watanni hudu masu zuwa.

"Najeriya ta jajirce kan kiwon lafiyar jama'a" - Pate

Wannan mataki zai kawo daukin gaggawa tare da nuna aniyar Najeriya na kafa tsarin samun kudade daga cikin gida don kula da lafiyar jama’a.

Punch ta rahoto ministan lafiya da walwala, Ali Pate, ya ce amincewar ta nuna jajircewar Najeriya wajen tabbatar da samun magani ba tare da tangarda ba.

"Wannan kudin zai taimaka wajen tabbatar da cewa masu cutar kanjamau na samun magani a koda yaushe ba tare da tsaiko ba," in ji Pate.

Kara karanta wannan

Bayan dakatar da shi daga masallaci a Kano, DSS ta gayyaci Sheikh Bin Uthman

Gwamnati ta kafa kwamitin gudanar da tsare-tsare

Ministan ya bayyana cewa FEC ta kafa kwamiti da aka hada da wakilai daga ma’aikatun kudi, kasafi, tsaro, muhalli da gwamnonin Najeriya don tsare-tsare.

"Manufarmu ita ce mu tabbatar da cewa babu wani dan Najeriya da zai rasa magani a wannan lokacin da ake samun canje-canje a duniya," in ji Pate.

Ya kara da cewa, duk da irin tallafin da Amurka ta bayar a shekaru 20, Najeriya na kokarin gina tsarin kiwon lafiya mai dorewa daga cikin gida.

Masu kanjamau na neman daukin gaggawa a Najeriya

A wani labarin, mun ruwaito cewa mutane sama da miliyan uku ke dauke da kwayar cutar HIV a Najeriya, amma kimanin 900,000 ne kawai ke samun magani.

Hukumar NACA ta bayyana cewa yawancin masu dauke da cutar a Najeriya ba sa samun magani saboda raguwar tallafin da ake samu daga kasashen waje.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.