Labari mai dadi: Kasar Amurka ta kulla yarjejeniyar dala miliyan 10 da jahar Kebbi don inganta noma
Na duke tsohon ciniki, kowa ya zo duniya kai ya tarar, wannan shine kirarin noma, wanda bahaushe yace shine tushen arziki, wannan sana’ar itace sana’ar da aka fi sanin jama’an Arewacin Najeriya na yi, musamman jama’an jahar Kebbi.
Kamfanin dillancin labaru, NAN, ta ruwaito gwamnatin kasar Amurka ta kulla wata yarjejeniya tsakaninta da gwamnatin jahar Kebbi don habbaka harkokin noma a jahar ta hanyar kashe makudan kudade da suka kai dala miliyan goma.
KU KARANTA: Rikicin jahar Benuwe: Yan ta’adda sun halaka jami’an dansanda da mutane 2 a Zaki Biam
A ranar Alhamis, 18 ga watan Oktoba ne aka kulla wannan yarjejeniya inda gidauniyar kasar Amurka dake kula da cigaban nahiyar Afirka a karkashin jagorancin Mista C.D Glin ya rattafa hannu akan yarjejeniyar, yayin da kwamishinan noma na jahar Kebbi, Attahiru Mashido ya rattafa hannu a madadin jahar.
Glin yace gidauniyar ta shirya tsaf don hada kai da kasashen Afirka wajen zuba jari a harkar noma tare da inganta harkar ta hanyar zamanantar da ita. A yayin kulla yarjejeniyar, Glin yace gidauniyar za ta samar da dala miliyan biyar, yayin da jahar Kebbi zata samar da dala miliyan biyar.
Majiyar NAIJ.com ta ruwaito Glin yana cewa a karkashin yarjejeniyar ta shekaru biyar, za’a samar ma kananan manoma da ingantaccen iri, tare da horas dasu akan hanyoyin noman zamani.
“Wannan yarjejeniyar zata mayar da hankali ne akan noman shinkafa, gyada da kiwon shanu domin samun madara, manufar wannan alakar itace don fadada kasuwancin kayan noma a jahar Kebbi, tare da kara yawan amfani gona da manoman jahar suke samu.
“Gidauniyarmu za ta samar da dala miliyan daya a duk shekara na tsawon shekaru biyar don samar da ingantaccen iri, tare da kayan aiki na zamani da koyar da dabarun noman zamani a karkashin sa’idon wata kungiyar Diamond Development Initiative.” Inji shi.
A nasa jawabin, gwamnan jahar Kebbi, Atiku Bagudu ya bayyana yarjejeniyar a matsayin mataki mai kyau da zai inganta tare da habbaka harkokin noma a jahar Kebbi. “Gwamnatin jahar Kebbi zata tabbatar da wannan yarjejeniya don samar da ayyukan yi ga talakawa gajiyayyu.
“Haka zalika gwamnatin Kebbi ta ware wasu kudade na daban don daukan amfanin gonan daga gonaki zuwa kasuwanni, haka zalika hakan zai bada damar ganawa da manoman shinkafa, masu sarrafa nona da masu soya kuli kuli.” Inji shi.
Ku biyo mu a https://facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/legitcomhausa
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng