Jerin Jihohi 11 mafi yawan masu cutar Kanjamau a Najeriya
A wani bincike da aka gudanar tun a watan Nuwamba na shekarar da ta gabata ya bayyana jerin wasu jihohin Najeriya mafi tarin masu dauke da cutar kanjamau wadda ke karya garkuwar jiki ta dukkan wani bil Adama mai dauke da ita.
Akwai dubunnan mutane ma su dauke da cutar Kanjamau a Najeriya, yayin da wasu ta kar su wasun su kuma su na nan a raye cikin wani hali na zaman jiran wa'adi.
Ga duk mai ganin cewa ko kuma tunani cutar kanjamau watau HIV/AIDS karya ce, to kuwa ya tafka babban kuskure kuma ya kamata ya tashi ya farka ya san ina ya dosa.
A sanadiyar wannan dalili ya sanya Legit.ng ta ke shawartar al'umma da su tashe tsaye su nemi kariyar kamuwa da cutar Kanjamau wajen mu'amalantar jama'a da ababen zamantakewa ta rayuwa.
KARANTA KUMA: Satar wayar Salula ta yi sanadiyar rasa hannayen wani Almajiri a jihar Gombe
Majalisar dinkin duniya ta sirranta jihohi mafi tarin ma su dauke da cutar kanjamau a Najeriya, sai dai hukumar rage yaduwa da ita watau NACA (National Agency for the Control of AIDS) ta bayyana su karara domin al'umma su dauki izina wajen kiyaye kawunan su.
Jaridar domin kawar da shakku ta kawo muku jerin jihohi 11 mafi tarin masu dauke da cutar a Najeriya kamar haka:
1. Jihar Ribas
2. Jihar Taraba
3. Jihar Kaduna
4. Jihar Nasarawa
5. Birnin tarayya Abuja
6. Jihar Akwa Ibom
7. Jihar Sakkwato da Oyo
8. Jihar Yobe
9. Jihar Cross River
10. Jihar Ondo
11. Jihar Edo
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng