Daga Fara Mulki Trump Ya Tono Badakalar COVID 19, Ya Yi Baram Baram da WHO
- Donald Trump, ya sanar da cewa Amurka za ta fice daga Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), yana zargin hukumar da gazawa wajen magance COVID-19
- WHO ta bayyana damuwarta game da ficewar kasar Amurka, wadda ita ce babbar mai bada gudummawa, tana mai fatan samun damar tattaunawa domin gyara lamarin
- Masana sun bayyana cewa ficewar Amurka na iya barazana ga shirye-shiryen WHO na yaki da tarin fuka, HIV/AIDS, da sauran matsalolin lafiya a sassan duniya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
America - Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya sanar da cewa Amurka za ta fice daga Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO).
Donald Trump ya dauki matakin ne yana mai zargin hukumar da sanya tasirin siyasa daga wasu ƙasashe da kuma neman kuɗi masu yawa daga Amurka fiye da sauran ƙasashe.

Asali: Facebook
Rahoton Reuters ya nuna cewa Trump ya bayyana haka ne a lokacin da ya rattaba hannu kan dokar ficewa daga WHO jim kadan bayan rantsar da shi a wa’adi na biyu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hukumar WHO ta bayyana cewa tana fatan Amurka za ta sake duba wannan matsaya, tana mai cewa lamarin zai iya shafar shirye-shiryen kiwon lafiya a duniya.
Zargin gazawar WHO wajen kula da COVID-19
Trump ya zargi WHO da gazawa wajen yaki da cutar COVID-19 da sauran matsalolin lafiya na duniya, yana mai cewa hukumar ta yi ƙasa a guiwa wajen dakile tasirin ƙasashe kamar China.
Ya kara da cewa Amurka na bada gudummawa mai yawa fiye da kima ga WHO, wanda hakan ya sa ya ga dacewar ficewa domin kare muradun kasar.
Tasirin ficewar Amurka ga kiwon lafiya
Rahotonni sun nuna cewa Amurka ce babbar mai tallafawa WHO, tana bada kusan kashi 18% na kasafin kudin hukumar.
Majalisar dinkin duniya ta wallafa cewa ficewar Amurka na iya shafar shirye-shiryen yaki da cututtuka kamar tarin fuka, cutar kanjamau, da sauran matsalolin gaggawa.
Masana kiwon lafiya na cikin gida da na waje sun bayyana damuwarsu kan ficewar, suna masu cewa hakan zai kawo cikas ga kokarin WHO na kula da lafiyar al’ummomi.
Martanin kasashe kan matakin Trump
Hukumar WHO ta musanta zargin Trump na nuna bangaranci, tana mai cewa tana ci gaba da matsa wa China lamba domin samar da bayanai kan tushen cutar COVID-19.
Kasar Jamus, wadda ita ce mai bayar da gudummawa ta uku mafi girma ga WHO, ta bayyana fatan samun damar tattaunawa da Trump domin hana ficewar.
Haka zalika, Gidauniyar Bill da Melinda Gates ta bayyana cewa za ta ci gaba da tallafawa WHO wajen karfafa ayyukan kiwon lafiya maimakon raunana su.
Ficewar Amurka, wadda za ta fara aiki bayan watanni 12, na nufin Amurka za ta dakatar da dukkan gudummawar kudi da kuma dangantakar aiki da hukumar.
Faransa za ta horas da 'yan Najeriya
A wani rahoton, kun ji cewa kasar Faransa ta sanar da shirin tallafawa tarayyar Najeriya wajen habaka ilimin ma'adanai.
Rahotanni sun nuna cewa Faransa za ta sanya Najeriya cikin kasashen Afrika da suke cin gajiyar tallafin horas da masana kan ma'adanai.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng