Sabbin mutane 108 sun sake kamuwa da kwayar cutar covid-19 a Najeriya, jimilla 981
An samu karin sabbin mutane 108 da su ka kamu da kwayar cutar coronavirus a ranar Alhamis, kamar yadda hukumar shawo kan cututtaka ma su yaduwa ta kasa (NCDC) ta sanar.
Jimillar mutanen da aka tabbatar su na dauke da kwayar cutar a Najeriya ya zama 981.
A cewar NCDC, mutum 78 ne su ka kamu da kwayar cutar a Legas, 14 a Abuja, da mutum 5 a jihar Ogun.
An tabbatar da samun mutum 4 a jihar Gombe, karin mutum 3 a jihar Borno da mutum biyu a jihar Akwa Ibom. An samun mutum dai - dai a jihohin Kwara da Filato.
Ya zuwa yanzu annobar cutar covid-19 ta hallaka mutane 31 a Najeriya, yayin da aka sallami mutum 197 bayan an tabbatar da warkewarsu.
Ga jerin jihohi da adadin mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar covid-19 ya zuwa yanzu;
Lagos-582
FCT-133
Kano-73
Ogun-29
Katsina-21
Osun-20
Oyo-17
Edo-17
Borno-12
Kwara-11
Akwa Ibom-11
Kaduna-9
Gombe-9
Bauchi-8
Delta-6
Ekiti-4
Ondo-3
Rivers-3
Jigawa-2
Enugu-2
Niger-2
Abia-2
Benue-1
Anambra-1
Sokoto-1
Adamawa-1
Plateau-1
Legit.ng ta wallafa cewa shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya aika sakon fatan alheri ga dukkan Musulman Najeriya da na duniya baki daya a yayin da za su fara azumin kwana 30, biyo bayan ganin watan Ramadan.
DUBA WANNAN: Gwamnan PDP ya bayar da umarnin yin bulala ga duk wanda aka gani babu takunkumi a jiharsa
"Ina taya duk Musulmi muranar zuwan azumin watan Ramadan, watan rahama, jin kai da taimakon mabukata," a cewar Buhari, kamar yadda kakakinsa, Mallam Garba Shehu, ya fada.
Shugaba Buhari ya bayyana azumin shekarar 2020 a matsayin mai cike da kalubale, saboda ya zo a cikin annobar da ta yadu zuwa kasashen duniya 200, lamarin da ya sa kasashe daukan tsauraran matakai.
A cewar shugaba Buhari, kusan duk kasashen duniya sun shawarci jama'arsu a kan su kauracewa taron jama'a da yawa, su gudanar da salloli da addu'o'i a gidajensu.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng