Soyayya Ta Kwashi Wani Matashi Yayin Da Ya Siyawa Budurwarsa Fili Da Duniyar Wata

Soyayya Ta Kwashi Wani Matashi Yayin Da Ya Siyawa Budurwarsa Fili Da Duniyar Wata

  • Duniya da fadi, wani matashi ya sha zumar soyayya inda ya rikice kan budurwar don burgeta a duniya
  • Matashin mai suna, Sohib Ahmed ya siyawa budurwarsa makeken fili a duniyar wata zabar sonta da ya ke
  • Matashin ya sayi filin ne daga Hukumar kula da filaye ta Kasa da Kasa da ke kula da filayen duniyar wata

Pakistan – Abin mamaki ba ya karewa a duniya yayin da wani matashi soyayya ta kwashe shi ya siya wa budurwarsa fili a duniyar wata.

Matashin wanda dan kasar Pakistan ne ya sayi filin ne mai girman eka daya don burge budurwar tasa.

Matashi ya siya wa budurwarsa fili a duniyar wata
Soyayya Ta Kwashi Wani Matashi Yayin Da Ya Burge Budurwarsa. Hoto: Daily Pakistan.
Asali: Facebook

Nawa matashin ya sayi filin a duniyar wata?

An bayyana sunan matashin da Sohib Ahmed wanda aka ce ya sayi filin kan makudan kudade har Dala 45 daga wata Hukuma ta Filayen Kasa da Kasa da ke kula da filayen duniyar wata.

Kara karanta wannan

Budurwa 'Yar Najeriya Ta Shiga Bakin Ciki Bayan Siyar Da Wayarta Don Saurayinta, Bidiyon Ya Yadu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Aminiya ta tattaro cewa matashin ya sayi filin a wani yanki na duniyar wata da ake kira ‘Sea of Vapour’.

Hukumar ta wallafa a shafinta na Twitter inda ta ce an lamuncewa mutane su mallaki filaye a duniyar wata don samun kudaden shiga ga duniyar.

Hukumar ta ce an kulla yarjejeniya wacce za ta bai wa wasu tsirarun mutane mallakar filaye don samun kudaden da za a gudanar da harkokin da ke bukatar kudade a duniyar wata.

Meye martanin budurwar kan siyan filin a duniyar wata?

Matashin ya ce ya kwaikwayi jarumin ‘Bollywood’ Sushant Singh da ya sayi fili a duniyar wata a shekarar 2018 a wani yanki da aka kira Mare Muscoviense.

Shi ma jarumin ya sayi filin a wurin hukumar kula da rijistar filayen sararin samaniya, Daily Pakistan ta tattaro.

Kara karanta wannan

“Ba Zai Ci Amana Ba”: Budurwa Yar Najeriya Ta Yi Caraf Da Masoyinta Da Tsurut Kamar Karamin Yaro

A bangarenta, budurwar matashin mai suna Madiha ta ce kawayenta sun yi mamakin yadda ta ke fada musu cewa saurayin ya siya mata fili a can.

Madiha ta fadawa Samaa TV cewa:

“Lokacin da na ke fada musu labarin filin ba su yarda ba, gani su ke wasa na ke, sai da na nuna musu takardun filin kafin su ka yarda.”

Ta bukaci duk wani da zai auri wata daga cikin kawayenta shi ma ya siya mata fili a duniyar wata.

Saurayi ya hana budurwarsa shiga gidansa bayan tazo 'yar bazata

A wani labarin, wani matashi ya hana budurwarsa shiga gidansa bayan ta kawo ziyara 'yar bazata.

Saurayin ya yi haka ne saboda budurwar ta zo tun daga Legas zuwa Ilorin ba tare da ya sani ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel