Saurayi Ya Hana Budurwa Shiga Gidansa Bayan Ta Kai Masa Ziyarar Bazata, Ya Mata Bidiyo

Saurayi Ya Hana Budurwa Shiga Gidansa Bayan Ta Kai Masa Ziyarar Bazata, Ya Mata Bidiyo

  • Wani dan Najeriya ya hana budurwarsa shiga gidansa bayan ta kawo masa ziyarar bazata
  • Ba tare da ya yi la'akari da cewar daga Lagas ta fito zuwa Ilorin ba, matashin ya horar da ita kan kin gaya masa cewar tana hanya
  • Ga mamakinta, ya ciro wayarsa sannan ya dunga yi mata bidiyo, yana mai cewa dole ta koma gidan iyayenta

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Wani dan Najeriya, @sauceprince_takingover, ya koyawa budurwarsa hankali bayan ta yi tattaki daga Lagas zuwa Ilorin domin kai masa ziyara ba tare da ta sanar da shi ba.

Ba tare da ya yi mata maraba da zuwa ba, matashin ya nemi jin ba'asin mai ta zo yi a wajensa sannan ya caccaketa kan kin kiransa ko aika masa da sakon tes kafin ta zo.

Saurayi ya hana budurwa shiga dakinsa
Saurayi Ya Hana Budurwa Shiga Gidansa Bayan Ta Kai Masa Ziyarar Bazata, Ya Mata Bidiyo Hoto: @sauceprince_takingover
Asali: TikTok

Yayin da ya datse kofarsa da makulli, ya umurceta da ta koma gidan iyayenta domin shi ba zai bude mata kogfarsa ba.

Kara karanta wannan

“Miliyan 4 Aka Biya Ni”: Matashi Da Ya Rikide Ya Koma Mace Ya Yi Tafiyar Rangwada Da Takalma Masu Tsini, Bidiyon Ya Girgiza Intanet

"Kawai kin dauko jaka daga Lagas kin tawo Ilorin. Jirgin sama ma ta shiga. Jirgin sama ne. Yallabai ba a yin haka," ya caccake budurwar.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Duk da rokon da budurwar ta yi masa ya yi kunnen uwar shegu da ita yayin da ya ci gaba da yi mata bidiyo, kafin ya shige ciki abinsa. A ciki ya ci gaba da sukarta kan kawo masa ziyarar bazata.

A cewarsa, ba a yin abubuwa haka. Bidiyonsa ya haddasa cece-kuce a TikTok.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

~Iilmomma ya yi martani:

"Akwai wata yarinya a cikin gidan nan."

Njoku Felicia ta ce:

"Ka bari ta koma gidan mahaifiyarta faaaa."

Tbusiness ta ce:

"Ka barta ta tsaya a waje."

MA MA ta ce:

"Yallabai ka barta ta shiga, da dogon bakinka."

Kara karanta wannan

Fitaccen Jarumin Fim Din Kannywood Ya Gamu Da Babbar Jarabawa, Ya Nemi a Taimaka Ma Sa

MAGIC FINGER ta ce:

"Kai mugu ne ka san ka yi mata wannan ta'asar sannan ka nemi ta fita saboda ka samu wata shiyasa ka ji kunya."

@ Mimi_Beauty093 ta ce:

"Baka da hankali dan uwa... Ina zuwa gidan saurayina ba tare da na sanar masa ba kuma ya kan ji dadin ganina ba tare da wata tambayar dalili ba."

Matar aure ta isa wajen bikin mijinta, aminiyarta ce amarya

A wani labari na daban, mun ji cewa an sha yar diraba a wajen sahagalin wani aure bayan uwar gida ta isa wajen da mijinta ke kara aure.

Ga mamakinsa sai ta ga cewa ashe ma aminiyarta ce amaryar da yake karawa lamarin da ya jefa ta cikin wani yanayi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel