Saurayi ya kashe budurwarsa saboda an hana shi soyaya da ita

Saurayi ya kashe budurwarsa saboda an hana shi soyaya da ita

Wani matashi mai shekaru 23 dake zaune a Owode-Ijako a karamar hukumar Ado-Oda/Ota na jihar Ogun, Salaudeen Issa ya fada hannun Yan sanda inda ake zarginsa ta kashe budurwarsa mai suna Kemi Ilo.

An ce wai wanda ake zargin yayi amfani da adda ne inda ya sare Kemi a kai misalin karfe 4 na asubahin ranar Lahadi inda ya bar ta kwance cikin jini kamar yadda muka samo a jaridar Punch.

An gano cewa masoyan sun sami rashin jituwa a kwanakin baya kafin harin ya faru, har ta kai ga cewa mahaifiyar budurwar (Kemi) ta gargadi saurayin ya dena kusantar diyarta inda shi kuma ya dau alwashin daukan mataki akan budurwar.

Saurayi ya kashe budurwarsa saboda an hana shi soyaya da ita

Saurayi ya kashe budurwarsa saboda an hana shi soyaya da ita

DUBA WANNAN: An damke wani dan shekaru 22 da laifin yiwa yar shekara 13 fyade

Wannan barzanar da saurayin yayi wa Kemi ne ya sanya ta kasa kwana a dakinsu kuma tayi shawarar kwana a dakin kawarta mai suna Maryam saboda gudun fitina. Kawar nata mai suna Maryam itace diyar mai gidan da su Maryam ke haya.

Wani mazaunin gidan mai suna Femi ya shaidawa manema labarai cewa Kemi tana sharbar barcinta yayinda wani mutum da ake kyautata zaton Issa ne ya sulalo cikin dakin kuma ya sare ta da adda kuma ya ranta a na kare.

Ya cigaba da cewa daga baya an kai Kemi asibiti har guda biyu amma basu karbe ta ba, ana hanyar kaita asibitin koyarwa na jami'ar Legas ne ta rasu.

Femi ya kara da cewa mosayan biyu sun saba rikici tsakaninsu amma daga baya su shirya. Yace akwai lokacin da suka sami rashin jituwa sai Issa yazo gidan amma bai sami Kemi amma yayi amfani da reza ya raunana jaririnta da ke barci a dakinta.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel