Budurwa Ta Shiga Kunci Bayan Siyar Da Wayarta Don Daukar Saurayinta Wurin Cin Abinci, Ya Yaudare Ta

Budurwa Ta Shiga Kunci Bayan Siyar Da Wayarta Don Daukar Saurayinta Wurin Cin Abinci, Ya Yaudare Ta

  • Wata budurwa 'yar Najeriya ta shiga bakin ciki bayan yiwa saurayinta goma ta arziki amma ya yaudare ta
  • Duk da haka sai da saurayin ya yaudare ta inda ya fara neman kawarta ta kut-da-kut
  • Mutane da dama sun so tausaya mata amma da su ka ji farashin fita shakatawa da ita, sai su ka ce Allah ya kara

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Wata budurwa ta bayyana yadda saurayinta ya yaudare ta bayan ta siyar da wayar ya don ta burge shi.

Ta ce abin bakin cikin ma shi ne yadda ya koma neman kawarta wacce ita ce babbar kawarta.

Budurwa ta siyar da wayarta don sautayi, ya yaudare ta
Budurwa Ta Shiga Kunci Bayan Saurayinta Ya Yaudare Ta. Hoto: @salina_sunshine.
Asali: TikTok

Wani matashi mai suna @salina_sunshine ya wallafa hakan a TikTok wanda ya ke hira da 'yan mata.

A wani bidiyon da ya wallafa an gano wata budurwa na bayyana yadda ta siyar da wayar ta don siya wa saurayinta sabuwar waya.

Kara karanta wannan

“Ba Zai Ci Amana Ba”: Budurwa Yar Najeriya Ta Yi Caraf Da Masoyinta Da Tsurut Kamar Karamin Yaro

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ta ce duk da sadaukarwar da ta yi masa sai da ya ci amanar ta wurin neman kawarta ta kut-da-kut.

Mutane da dama sun yi martani kan wannan labari inda su ke cewa ai mata ba abin tausayi ba ne tun da idan ba ka da dubu 100 zuwa 200 ba za ka iya fita da su ba.

Ku kalli bidiyon a kasa:

Legit ta tattaro muku wasu daga cikin martanin jama'a kan bidiyon:

Georgebrain:

"Na gane dalilin da ya sa su ke cin karin kumallo."

Arikeh_baby:

"Yawan kallon wasan kwaikwayonsu ya yi yawa, wurin cin abinci na sarakuna."

Immaculate1:

"Wurin cin abinci masu zaman kansu kaman babansu ne ya mallaka."

user5708245101145:

"Nagode wa Allah wautata ba ta kai haka ba."

Shalom:

Kara karanta wannan

Matashi Ya Siyawa Budurwa Sabuwar Marsandi, iPhone 15 Da Fili, Bidiyon Ya Girgiza Intanet

"Naira dubu 200?, Wasu daga cikinmu ba mu taba fita daga gidajenmu ba."

Wurld:

"A baya ina tausayinsu amma daga baya na bari saboda tsadar nemansu, tabbas sun cancanci karin kumallo."

Call me when it's best:

"Ina ma ace wani ya taimaka min naga irin wadannan gayun, sun yi bajinta, a baya ina tausayinsu."

Bidiyon matashin da ke ciyar da ragonsa da biredi da shayi

A wani labarin, an wallafa wani bidiyo inda wani matashi ya ke ririta ragonsa kamar dan Adam.

Matashin na ciyar da rogin da biredi da shayi bayan ya wanke masa baki da buroshi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel