Ciwon Daji Na Mama: Maganin Yana Tare Da Mazajenku, Kwarariyya Ta Shawarci Mata
- Charity Twumasi Ankrah, kwararriya a bangaren lafiya ta shawarci mata kan hanyoyin da za su iya bi don kare kansu daga ciwon sankarar mama
- Ankrah ta shawarci matan su rika shayar da yayansu mama ko kuma mazajensu na aure a lokacin da ba su shayar da yara don hakan na da alfano ga lafiyarsu
- Shugaban na Chartma Herbal Health Centre ta kuma shawarci mata su tafi asibitoci don a duba su musamman a watan Oktoba da duniya ta ware don wayar da kai kan cutar kansar sankarar mama
Ghana - Kwararriya a bangaren lafiya kuma shugaban cibiyar Lafiya ta Chartma Herbal Health Centre ta bukaci maza su rika shan mama a cikin watan Oktoba a wani mataki na wayar da kai game da kansar mama.
An ware watan Okotoban kowace shekara a matsayin watan wayar da kai kan cutar sankarar mama a faɗin duniya.
Charity Twumasi Ankrah a hirar da ta yi da KMJ a shirin Prime Morning a ranar Talata ta yi bayanin cewa shan mama na taimakawa rage wa mata kamuwa da kansar mama.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A cewarta, yana da muhimmanci ga mace ya zamana ana shan mamanta don yana kara lafiya.
Ta ce:
"Shayar da yaran ku mama yana da matukar muhimmanci. Shi yasa idan mace bata haihu ba, abin damuwa ne, akwai damuwa don akwai amfani a shayarwa."
Kwararriyar ta kara da kira ga maza wadanda ba su yin hakan a baya su daure su ko na wannan watan ne domin matansu su amfana a yayin da ake bikin watan wayar da kai game da kansar nono.
Hakazalika, kwararriyar a bangaren lafiya ta nuna cewa ba wai kullum bane ake bukatar haka, sai dai lokaci zuwa lokaci.
Ta kuma gargadi maza su dena yamutsawa matansu mama don hakan na iya musu ciwo, tana mai cewa ba 'balan-balan bane'.
Kada ku ji tsoron yanke mama don kare sauran jikinku, Ankrah ta shawarci mata
Charity Ankrah ta kuma shawarci mata wadanda suka kamu da kansa su yanke nonon da ya kamu don kare sauran jikinsu. Ta ce hakan ba karshen rayuwa bane.
Ta ce:
"Kamuwa da kansar mama ba karshen rayuwa bane. Ya kamata in iya cire wanda ya kamu don ceton rayuwa na. Ba zai yi dadi in cire dukkan biyun ba, amma zan iya cire daya."
Ta kuma shawarci mata su cire kunya su rika zuwa asibiti don a tantance su idan kuma ta kama a cire su daure a yi hakan.
Ankrah: A dena tsangwamar mata da aka yanke wa mama saboda kansa
Range Rover Nake So: Miji Ya Gwangwaje Matarsa Da Motar Wasan Yara Yayin da Ta Dame Shi Ya Siya Mata Mota
Kwararriyar ta kuma yi kira ga al'umma su dena tsangwamar matar da aka yanke wa mama saboda kansa.
Daga karshe ta shawarci mata su tafi asibiti mafi kusa da su a cikin watan Oktoban a duba su a yayin da ake bikin wayar da kan na kansar mama.
Abin da kwararriyar ma'aikaciyar jinya a Najeriya ta ce game da alakar kansar mama da bawa mazaje mama su sha
Wakilin Legit.ng Hausa ya tuntubi wata kwararriyar ma'aikaciyar jinya, Hauwa Abdullahi da ke aiki a asibitin koyarwa na Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria don samun karin haske kan alakar shan mama da cutar kansar mama.
Hauwa ta ce ikirarin cewa barin maza su rika shan mama yana rage yiwuwar kamu da kansa ba shi da madafa a kimiyyance, shayar da yara ne ke iya rage yiuwuwar kamuwa da kansar.
A cewarta:
"Ikirarin cewa idan maza na shan maman matansu yana rage yiwuwar kamuwa da kansar mama ba shi da tushe a bincike na kimiyya.
"Amma, zai iya taimakawa wurin gano kansar da wuri, don mijin zai iya gano canji a yanayin maman hakan kuma ya sa matar ta tafi asibiti a duba ta."
Shayar da yara mama ne ke rage yiwuwar kamuwa da kansar mama
"Amma shayar da yara mama da masu jego ke yi na rage yiwuwar kamuwa da cutar kansar mama da kashi 4.3 cikin 100 duk wata 12 da aka yi ana shayar da yaro."
Dawisun Namiji Mai Kyawawan Mata 8 Ya Ce Wasu Cikinsu Na Kishi Da Shi, Hotuna Sun Bayyana
A wani rahoton, Dan kasar Brazil wanda ya auri mata takwas ya magantu kan rayuwa aurensa, yana mai cewa wasu cikin matansa sun ce ba su son ya yi tumbi.
Arthur O Urso ya yi suna ne a shekarar 2021 bayan ya auri mata guda takwas a Sao Paulo, Brazil.
Asali: Legit.ng