Range Rover Nake So: Miji Ya Gwangwaje Matarsa Da Motar Wasan Yara Yayin da Ta Dame Shi Ya Siya Mata Mota

Range Rover Nake So: Miji Ya Gwangwaje Matarsa Da Motar Wasan Yara Yayin da Ta Dame Shi Ya Siya Mata Mota

  • Wani mutumi ya haddasa cece-kuce bayan ya gwangwaje matarsa wacce ta nemi ya siyasa mata Range Rover da motar wasan yara
  • Mutumin ya bude kwalin kyautar da ya kawo mata yana mai cewa abun da ya iya siyo mata kenan, lamarin da ya cika matar da mamaki
  • Mutane da dama da suka yi martani ga bidiyon sun bayyana cewa sun so yadda matar ta karbi kyautar da zuciya daya

Wata matashiya ta wallafa dan takaitaccen bidiyo na abun da mahaifinta yayi a bikin zagayowar ranar haihuwar mahaifiyarta.

Kafin zuwan wannan rana, matar ta bukaci mijin nata da ya siya mata mota kirar Range Rover don raya wannan rana.

Mata da miji
Matar tace ta amshi motar da zuciya daya Hoto: TikTok/@emilykhani1
Asali: UGC

Mutumin ya gabatar mata da wata kyauta a kwali. Ya bude kwalin sannan ya nuna mata motar wasan yara. Mijin yace wannan ne Range Rover din da ya iya sama mata.

Kara karanta wannan

Wannan Shekarar Tazo da Albarka: Budurwar Da Tayi Wata 5 Tana Kwana a Kasa Ta Siya Sabon Gado Dal

Ta amshi Range Rover din da hannu bibbiyu

Yayin da komai ke gudana, matar ta rasa ta cewa inda ta saki baki tana kallon ikon Allah. Jim kadan bayan nan, sai matar ta rike motar wasan sannan tace ta amshe shi a matsayin ainahin Range rover din gaske da zuciya daya.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Mutane da dama da suka kalli bidiyon sun bayyana cewa sun gaza daina dariya kan wannan abun dariya da mutumin yayi da kuma martanin matar.

Kalli bidiyon a kasa:

Legit.ng ta tattaro wasu daga cikin martanin a kasa:

Osaseri81 ya ce:

“Na so martaninta, koda bai zamana abun da take so ba ta amshe shi hannu bibbiyu. Kyakkyawar mata.”

Diamond ta ce:

“Na so martaninta, kyakkyawan iyali,uwa mai zuciyar alkhairi ina sonta.”

Hassana Amadu ta ce:

“Da gaske cewa yayi zaki iya shiga uwargida.”

Kara karanta wannan

Idan Na Siya Dankareriyar Mota Kada Kuyi Mamaki, Budurwa ‘Yar Najeriya Da Ke Sana’ar Jari Bola

Mawins ta ce:

“Kyakkyawar mata, ki karba da zuciya daya haka zai kasance.”

Bidiyo: Wani Mutum Ya Yo Odar Gida Daga China, Ya Dasa Shi A Kan Filinsa

A wani labarin, wani mutum mai suna Zackary South, ya nunawa mutane hanyar da zasu bi wajen mallakar gida sukutum ba tare da amfani da bulo ko siminta ba.

A cikin wani bidiyo da ya yadu a TikTok, Zackary ya bayyana cewa ya shigo da wani gidan kwantena daga kasar China kuma ya yi odar gidan ne tsawon watanni uku kafin suka iso.

Lokacin da kwantenan ya izo wajensa, sai ya zamana gida ne mai dauka biyu da madafi da kuma bandaki bayan an hada shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel