Dalilin Da Yasa Na Saci Sabon Jariri A Asibitin ATBUTH Dake Bauchi

Dalilin Da Yasa Na Saci Sabon Jariri A Asibitin ATBUTH Dake Bauchi

  • Hukumar yan sandan jihar Bauchi ta bayyana matar da ta saci jariri a asibiti gaban yan jarida
  • Matar tayi nadamar abinda ta aikata kuma ta bukaci gwamnati ta sassauta mata wajen hukunci
  • Jami'an tsaro sun ceto yaro daya daga cikin tagwayen da ta sace a asibitin ATBU a Bauchi

Bauchi - Matar da ta sace jariri kwanakin baya a asibitin koyarwan Abubakar Tafawa Balewa ATBU dake Bauchi ta bayyana nadamarta bisa abin da ta aikata.

Matar mai suna, Sukyama Irmiya, yayinda aka bayyanata gaban manema labarai tace kunya ne yayi mata yawa saboda rashin samun haihuwa shiyasa ta yanke shawarar sace jaririn.

Ta bayana cewa har ga Allah ta yi niyyar kula da yaron kaman wanda ta haifa da kanta amma tana neman gafarar iyayen jaririn da kuma gwamnati, rahoton Tribune.

Ikrima
Dalilin Da Yasa Na Saci Sabon Jariri A Asibitin ATBUTH Dake Bauchi Hoto: tribune.com
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewarta,

"Na gane kuskure na, babu wanda zai fahimci halin da na shiga sai ya shiga irin halin. Yanzu ya gwammace in mutu da wannan hali na nike ciki."
"Ina neman gafara wajen iyayen da sauran mutanen da abin ya shafa, sannan ina neman yafiya wajen Ubangiji. Ita kuwa hukuma ina neman ta mini sauki. Na sa na aikata laifi, a yafe min."
"Kana ina kira ga mutane iri na kada su bari shaidan ya rudesu, shaidan ne ya jefa ni halin nan, su kusanci Allah don neman mafita daga cikin matsalolinsu."

An Ceto Jaririn Da Wata Mata Ta Sace A Asibitin ATBU Bauchi

A watan Satumba, hukumar yan sandan jihar Bauchi ta bayyana matar da ta saci jariri a asibiti gaban yan jarida

Matar tayi nadamar abinda ta aikata kuma ta bukaci gwamnati ta sassauta mata wajen hukunci

Jami'an tsaro sun ceto yaro daya daga cikin tagwayen da ta sace a asibitin ATBU a Bauchi.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel