'Yan Sanda Sun Kai Samame Mafakar Masu Aikata Muggan Laifuka, Sun Samu Gagarumar Nasara a Katsina

'Yan Sanda Sun Kai Samame Mafakar Masu Aikata Muggan Laifuka, Sun Samu Gagarumar Nasara a Katsina

  • Rundunar yan sandan Katsina tace ta kubutar da wasu mutane tara da ake kokarin safararsu bayan wani samame da ta kai mabuyar miyagu a Daura
  • An ceto mutanen wadanda duk mata ne a daidai lokacin da ake kokarin kaisu kasar Libya ta iyakar Nijar
  • Kakakin yan sandan jihar, Gambo Isah ne ya tabbatar da hakan a ranar Laraba, 6 ga watan Oktoba

Katsina - Rundunar yan sanda a jihar Katsina ta yi nasarar ceto akalla mutane tara yayin da ake kokarin safararsu zuwa wata kasar waje.

Channels TV ta rahoto cewa an ceto mutanen da abun ya ritsa dasu wadanda dukkansu mata ne a ranar 29 ga watan Satumban 2022 bayan rundunar yan sandan ta samu bayanan sirri.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun fusata, matar Atiku ta ba 'yar sanda ta rike mata jaka a wurin taro

Jami'an yan sanda
'Yan Sanda Sun Kai Samame Mafakar Masu Aikata Muggan Laifuka, Sun Samu Gagarumar Nasara a Katsina Hoto: Premium Times
Asali: UGC

A wani jawabi dauke da sa hannun kakakin rundunar, SP Gambo Isah, ya bayyana cewa jami’an yan sanda sun farmaki mabuyar miyagun a karamar hukumar Daura da ke jihar, inda anan ne aka tsare mutanen.

Ya kara da cewar, a yayin da ake gudanar da bincike, mutanen da aka ceto sun bayyana cewa wani direba ne ya dauko su daga jihar Kano zuwa Daura.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sun kuma bayyana cewa direban ya yasar da su sannan ya tsere bayan ya hango tawagar yan sanda.

Yan matan sun kuma bayyana cewa, suna a hanyarsu ta zuwa Libya ne ta iyakar Nijar kafin jami’an tsaro suka cafke su.

Wadanda aka ceto sun hada da Timilaye Ojo mai shekaru 26 daga jihar Lagas, Blessing Joseph mai shekaru 19 daga jihar Edo, Khadija Abdullahi mai shekaru 29 daga jihar Ondo.

Kara karanta wannan

Yadda na kwashe shekaru da dama ina jinyar mijina kan ciwon PTSD, Aisha Buhari

Sauran sune Safiyyat Ahmed mai shekaru 21 daga jihar Lagos da kuma Precious Nuhu mai shekaru 22 daga jihar Kaduna, Bolanle Adewusi mai shekaru 32 daga jihar Ogun

Sai Okpoekwu Eunice mai shekaru 28 daga jihar Enugu, Kabirat Azeez mai shekaru 19 daga jihar Ondo da kuma Taiwo Adeolo mai shekaru 27 daga jihar Ondo.

Rundunar yan sandan tace ana nan ana ci gaba da gudanar da bincike da nufin kama miyagun da suka tsere, rahoton TheCable.

Mutane 3 Sun Mutu, Wasu Da Dama Sun Jikkata Yayin da Mayakan Boko Haram Suka Farmaki Borno

A wani labari na daban, mun ji cewa mayakan kungiyar ta’addanci na Boko Haram sun kashe akalla mutum uku a wani sabon farmaki da suka kai garin Njilang da ke karamar hukumar Chibok a jihar Borno.

Wata majiya ta tattabatar da faruwa lamarin ga Channels TV a wata hira ta wayar tarho a ranar Talata, 4 ga watan Oktoba.

Kara karanta wannan

Bayan Watanni Uku, Sabbin Bayanai Sun Fito Kan Fursunonin da Suka Gudu Daga Gidan Yarin Kuje

Majiyar ta ce mayakan sun farmaki sabuwar hanyar Maiduguri –Damboa da aka bude kwanan nan a tsakar daren yau Talata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel