Dawisun Namiji Mai Kyawawan Mata 8 Ya Ce Wasu Cikinsu Na Kishi Da Shi, Hotuna Sun Bayyana

Dawisun Namiji Mai Kyawawan Mata 8 Ya Ce Wasu Cikinsu Na Kishi Da Shi, Hotuna Sun Bayyana

  • Wani mutum dan kasar Brazil mai suna Arthur Urso, wanda ya yi fice saboda auren mata takwas, ya sanar da duniya cewa shi 'spornsexual' ne
  • Spornsexual kalma ce da ake amfani da shi don kwatanta namiji yawan ado, gyaran jikinsa da tsafta
  • Amma, Urso ya ce wasu daga cikin matansa ra'ayinsu ya banbanta kuma ba su cika son yana yawan mayar da hankali kan jikinsa ba

Dan kasar Brazil wanda ya auri mata takwas ya magantu kan rayuwa aurensa, yana mai cewa wasu cikin matansa sun ce ba su son ya yi tumbi.

Miji da matansa takwas
Mutumin Da Ke Da Kyawawan Mata 8 Ya Ce Wasu Cikinsu Na Kishi Da Shi, Hotuna Sun Bayyana. Hoto: Arthur Urso.
Asali: UGC

Wasu cikin matan Arthur suna son ya rika motsa jiki da kula da sifansa

Arthur O Urso ya yi suna ne a shekarar 2021 bayan ya auri mata guda takwas a Sao Paulo, Brazil.

Kara karanta wannan

Hotunan Yadda Aka Fallasa Wani Mutum Da Ke Bara Da Yara Masu Ciwon Ciki Na Karya A Legas

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

The Mirror ta rahoto cewa a baya-bayan nan Urso ya bayyana kansa a matsayin 'spornsexual' - kalma da aka fara amfani da shi a shekarar 2010 don siffanta na miji kai kakarfan jiki, caba ado da tsafta.

Maza da dama sun ce Urso na rayuwa a 'aljannar duniya' tare da matansa, amma magidancin ya ce abu bane mai sauki kiyayye sharrudan da matansa ke gindiya masa.

Arthur ya fada wa The Mirror cewa:

"Suna son in cigaba da motsa jiki kada, idan ba haka ba su rika korafi."

Domin kada tumbinsa ta yi girma, mijin matan takwas ya ce ya kan yawan zuwa wurin motsa jiki wato gym kuma ya rage cin na'ikan abinci masu sa kiba.

Ya ce:

"Bana cin gluten, lactos, har burodi da taliya."

Kara karanta wannan

Tashi Ka Nemi Abun Yi: Fusatattar Matar Aure Ta Dangwararwa Da Miji Kwano Babu Abinci

Wasu ba su son ya rika yawaita ado

Yayin da wasu matan Urso suna sha'awan jikinsa irin na masu guje-guje, shi kansa yana jin dadin kalon siffansa a madubi, wani hali na spornsexuals.

Amma, Urso ya ce wasu matansa ba su cika son su ga yana yawan kwalliya da kula da gyaran jiki ba.

Ya bayyana cewa:

"Wasu daga cikinsu ba su son su ga ina yawan gyaran jiki - wasun su na kishi."

Da farko, Urso ya fara auren Luana Kazaki, suka rika wallafa bidiyo tare inda suka samu kudi $73,000 (N31,405,330) duk wata a OnlyFans.

A bara, amma, Urso, ya yanke shawarar auren wasu matan bakwai don nuna rashin amincewarsa da 'auren mace guda'. Auren bai halasta ba a doka saboda haramun ne auren maci fiye da daya a Brazil.

"Daga Yar Aiki Ta Zama Matan Mai Gida": Budurwa Ta Girgije A Bidiyo Don Farin Ciki

A wani rahoton, wata mata mai juna biyu ta bawa mutane labarin soyayyar ta mai ban mamaki.

Kara karanta wannan

Ta koma ga Allah: Bidiyon budurwar da ta ce sauranta watanni 7 a duniya ya jawo cece-kuce

A cewar matan mai suna simplisauce a TikTok, bayan ta kammala makarantar sakandare, zabi biyu da ta ke da shi sune zama yar aikin gida ko kuma bin mazaje.

Asali: Legit.ng

Online view pixel