Mun Kashe Dala Miliyan 10 Don Ciyar Da Ɗalibai Miliyan 10, In Ji Gwamnatin Tarayyar Najeriya

Mun Kashe Dala Miliyan 10 Don Ciyar Da Ɗalibai Miliyan 10, In Ji Gwamnatin Tarayyar Najeriya

  • Gwamnati Najeriya ta ce a halin yanzu ta kashe a kalla dalar Amurka miliyan 10 don ciyar da dalibai miliyan 10 a jihohin kasar
  • Mr Chris Ngige, ministan Kwadago da samar da ayyuka ne ya bayyana hakan a ranar Juma'a yayin da jakadar Amurka a Najeriya ta kai masa ziyara
  • Ngige ya ce gwamnatin Najeriya ta kirkiri shirin ne da nufin dakile bautar da kananan yara da ake yi musamman a yankunan karkara ta kuma ke bada ilimi kyauta

FCT Abuja - Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce ta kashe kimanin Dalar Amurka Miliyan 10 don ciyar da yaran Najeriya karkashin shirin National School Feeding Programme.

Wannan na cikin wani yunkuri ne na kawar da bautar da kananan yara a kasar, Premium Times ta rahoto.

Ngige
Najeriya Ta Kashe Dalar Amurka Miliyan 10 Don Ciyar Da Ɗalibai N10m, In Ji Gwamnatin Tarayya. Hoto: The Nation News.
Asali: Twitter

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Ɗan Takarar Shugaban Kasa Na Babban Jam'iyya Ya Bayyana Abu Guda Ɗaya Da Zai Gyara Najeriya

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Chris Ngige, ministan Kwadago da samar da ayyuka ne ya bayyana hakan yayin da ya karbi bakuncin jakadar Amurka a Najeriya, Mary Leonard, da wasu jami'an gwamnatin Amurka da suka kai masa ziyarar ban girma a ranar Juma'a.

Wannan na cikin sanarwar da Olajide Oshundun, shugaban sashin hulda da jama'a na ma'aikatar ya fitar.

Mr Ngige ya ce gwamnatin Najeriya ta ɓullo da shirin ciyar da yaran makarantar ne karkashin tsarin tallafawa marasa ƙarfi, don janyo yaran da ke aiki su dena su koma makaranta.

Gwamnati ta bullo da shirin ciyar da yara ne don dakile bautar da yara da tabbatar sun samu ilimi

Ya ce gwamnatin tarayyar ta kuma ɓullo da shirin yaki da talauci, wanda na daya cikin dalilan da yasa ake bautar da yara kanana a Najeriya.

Kara karanta wannan

A Shekaru 3 a Ofis, Mun Kammala Ayyuka Fiye da 2000 a Ma’ikatarmu – Isa Pantami

A cewarsa:

"Mun bullo da shirin ciyarwa na makarantu a kasar a karkashin tsarin tallafawa marasa galihu, da nufin dawo da yara makaranta.
"A halin yanzu, nuna ciyar da yara guda miliyan 10 a sassan kasar nan. Mun kashe kusan Dalar Amurka Miliyan 10 a wannan aikin.
"Mun kuma kara gina makarantu a yankunan da akwai yiwuwar a rika bautar da kananan yara mun kuma mayar da ilimin kyauta a dukkan kasar ta karkashin UBE da Dokar Kare Hakkin Yara."

Mun yi wa msu nakasa tanadi - Ngige

Ya cigaba da cewa:

"Ga masu nakasa kuma, mun gabatar da hukuma ta mutane masu nakasa, don basu kulawa wanda ya kamata.
"An yi hakan ne kada su rika ganin kaman suna da wata nakasa. Idan baka tallafawa mai nakasa ba, talauci kawai zai haifar."

Ministan ya kuma jinjina wa kasar Amurka bisa taimakon da ta rika bada wa a bangaren shawarwari a karkashin sashin Kwadago na Afirka ta Yamma.

Asali: Legit.ng

Online view pixel