Shaharariyar Jarumar Fina-Finan Indiya Ta Mayar Da Martani Ga Masu Sukar Ta Da Cewa Don Kudi Ta Auri Mijinta

Shaharariyar Jarumar Fina-Finan Indiya Ta Mayar Da Martani Ga Masu Sukar Ta Da Cewa Don Kudi Ta Auri Mijinta

  • Auren Mahalakshmi, shaharariyar jarumar fina-finai a kasar Indiya da sabon mijinta Ravindar Chandrasekaran ya dauki hankulan wasu mutane a shafukan sada zumunta
  • Daga cikin masu tofa albarkacin bakinsu kan auren, akwai masu ikirarin cewa Mahalakshmi ta auri Chandrasekaran ne saboda kudinsa ba don soyayya ba
  • Amma, jarumar da mijinta furodusa sun yi martani ga masu sukar auren inda suka ce soyayya ba ruwansa da siffa kuma Mahalakshmi ta ce tun kafin auren tana iya kula da kanta

Indiya - A cikin yan kwanakin nan ne aka daura auren shaharariyar jarumar fina-finai na Indiya, Mahalakshmi da furodusa, Ravindar Chandrasekaran.

Amma, wasu mutane a shafukan sada zumunta sun rika sukar Mahalakshmi kan cewa ta auri Ravinder ne saboda kudinsa.

Kara karanta wannan

Dan Najeriya ya jawo cece-kuce yayin da ya fara birgima a kasa lokacin da matarsa ta haihu

Jaruman Indiya
Sharrariyar Jarumar Fina-Finan Indiya Ta Mayar Da Martani Ga Wadanda Ke Cewa Don Kudi Ta Auri Mijinta. Hoto: @Lindaikeji
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ravindar shima ba su kyalle shi ba saboda yanayinsa da kibansa, wasu sun rika fadin maganganu marasa dadi gare shi.

Mahalakshmi wanda ta taba aure a baya, ta hadu da sabon mijinta ne yayin da suke aiki kan fim dinsa da zai fito.

Jaruman Indiya
Sharrariyar Jarumar Fina-Finan Indiya Ta Mayar Da Martani Ga Masu Sukar Ta Da Cewa Don Kudi Ta Auri Mijinta. Hoto: @Lindaikeji.
Asali: Twitter

Jaruman Indiya
Sharrariyar Jarumar Fina-Finan Indiya Ta Mayar Da Martani Ga Masu Sukar Ta Da Cewa Don Kudi Ta Auri Mijinta. hoto: @lindaikeji.
Asali: Twitter

Jaruman Indiya
Sharrariyar Jarumar Fina-Finan Indiya Ta Mayar Da Martani Ga Masu Sukar Ta Da Cewa Don Kudi Ta Auri Mijinta. Hoto: @lindaikeji.
Asali: Twitter

Martanin Mahalakshmi da Ravindar ga masu sukarsu

Ba tare da damuwa da sukar ba, amarya da angon sun yi bidiyo na kai tsaye a instagram suka mayar da martani kan masu sukar Ravinder.

Jarumar, ta ce bai dace a rika zagin kowa ba saboda sifarsa har da Ravinder.

Ravinder, a bangarensa ya yi martani cikin sassanyar yanayi ga masu sukarsa.

Ya ce:

"Wannan ba wai don ni furodusa bane na fim amma sai dai saboda ni mutum ne mai kiba kuma na auri kyakyawar mace, ya kara da cewa soyayya ba ruwansa da siffa."

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Shugaban Hukumar PSC, Musiliu Smith Ya Yi Murabus Daga Mukaminsa

Tun kafin in yi aure ina kula da da na ni kadai - Mahalakshmi

Baya ga bidiyon da suka yi a Instagram, Mahalakshmi ta kuma yi hira da Sun Television inda ta karyata cewa don kudin Ravinder ta aure shi.

A cewar jarumar, tana da kudinta kuma tana kula da danta ita kadai ba tare da neman tallafi daga wani ba.

Mahalakshmi ta ce da farko bata son aure. Amma, ta canja ra'ayinta bayan Ravindar ya yi mata tayi.

Kannywood: Wasu Shahararrun Jarumai Mata Da Aurensu Ya Mutu

Kowa yana yin aure ne don ya zauna har abada, amma bayan wani lokaci ana samu matsaloli iri-iri wadanda suke kawo cikas a auratayyar.

Ana samun mutuwar aure a wurin sanannun mutane na duniya, don haka ko a Najeriya ma ba a rasawa.

Akwai fitattun jarumai da suka yi aure kuma ya mutu wadanda suka ci gaba sana’o’i da sauran harkoki na rayuwarsu, ga wasu daga cikinsu kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel