Dan Najeriya Ya Tuntsure a Kasa Tsabar Dadi Saboda Matarsa Ta Sauka Lafiya a Asibiti

Dan Najeriya Ya Tuntsure a Kasa Tsabar Dadi Saboda Matarsa Ta Sauka Lafiya a Asibiti

  • Wani dan Najeriya ya shiga farin ciki da murnar zama uba, inda ya nuna wani hali mai ban mamaki a asibiti
  • Da aka bashi labarin matarsa ta sauka lafiya kalaua, cikin farin ciki da annaushuwa da durkusa har kasa ya godewa Allah
  • Daga nan ne fa ya yi wani abu, inda ya dinga birgima a kasa tsabar dadin da yaji, lamarin da ya bar mutane baki bude

Wani dan Najeriya ya nuna wani hali mai ban mamaki a asibiti yayin da ya gano matarsa ta haifi jaririnta lafiya.

Wani bidiyon da @saintavenue_ent1 ya yada a Instagram ya nuna lokacin da mutumin ya shiga asibiti duba matarsa.

Da farko dai gani aka yi mutumin ya durkusa kan gwiwowinsa sannan ya kai kansa ya yi sujudar godiya a kasa. Daga bisani, an ga ya fara birgima a kasa kamar karamin yaro yana dukan kasa da tafukan hannunsa.

Matashin da matarsa ta haihu ya jawo cece-kuce a Instagram
Dan Najeriya ya tuntsure a kasa tsabar dadi saboda matarsa ta sauka lafiya a asibiti | Hoto: @onlyrebeka
Asali: Instagram

Jama'ar dake cikin asibitin sun shiga mamaki, inda suka fara zura masa ido yayin da yake wannan bakuwar dabi'a.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A wani yanki na bidiyon kuwa, an nuna shi lokacin da yake rike da jaririn da aka haifa a cikijn tsumma.

Martanin 'yan soshiyal midiya

Jama'a a kafar sada zumunta sun bayyana martaninsu da ganin wannan matashi sabon uba.

Kalli bidiyon:

@lukingud123 yace:

"Da gani dan fari ne, don haka ka fada da namiji ne don mu tayaka murna."

@ayewumistephen yace:

"Farin cikin ba zai misaltu ba. Duk halin wahala da namiji ke ciki, kai dai jira ace matarsa na gadon haihuwa. Anan ne fa zaka ga yana kai komo kamar kujerar mai aski. Ina yiwa mata masu juna biyu fatan sauka lafiya."

@b_d_dream yace:

"Wannan bai ga komai ba ma. Kana farin ciki da kashe kudi? Basu fada maka ba da kyau ba."

@__randyy07 yace:

"Na shiga irin wannan yanayin a ranar Litinin lokacin da matata ta haifi diya mace."

@lookingforthewitch yace:

"Kaji jama'a da wasu shiritan martani ina ruwanku sun shirya ko basu shirya ba ku da baku shirya ba ina kuke yanzu? Ku daina wani tura baki abin da bai shafe ku ba.

Bidiyon Yadda Fasto Ya Jawo Cece-Kuce Yayin da Ya Daura Auren Wani Mutum da Mata Uku Nan Take

A wani labarin, wani cocin addinin kirista da ake kira Primitive Church ya daura auren wani mutum da amarensa har guda uku a nan take.

Sabanin wasu cocin addinin kirista, wannan coci dai na goyon bayan auren mace fiye da daya, kuma ya ba mambobinsa damar auren adadin matan da suke so.

A wani faifan bidiyon da Afrimax English ya fitar a YouTube, an ga faston cocin na daura auren Byamungu Kanjira Prosper tare da matansa uku da ya kawo domin ya aure su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel